Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-29@21:02:22 GMT

Gwamnatin jihar Kano ta hana zubar da shara a Titin Kotu

Published: 27th, February 2025 GMT

Gwamnatin jihar Kano ta hana zubar da shara a Titin Kotu

A kokarin da take yi na magance kalubalen muhalli da inganta ayyukan sarrafa sharar gida mai dorewa, gwamnatin jihar ta hana zubar da shara a filin titin kotu.

 

Wannan shawarar na da nufin hana yaduwar cututtuka da kuma kare lafiya da amincin mazauna da masu wucewa.

 

A yayin ziyarar da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Dr.

Dahiru Muhammad Hashim ya kai wurin ya bayyana damuwarsa kan illar muhalli da kiwon lafiya daga zubar da shara.

 

Ya jaddada kudirin gwamnati na samar da ingantattun dabarun sarrafa shara don kare lafiyar jama’a da muhalli.

 

Dokta Hashim ya ba da umarnin kwashe sharar da suka taru a yankin, sannan ya shawarci mazauna yankin da su rika zubar da sharar su a wurin da aka kebe a garin Sallari.

 

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga kokarin gwamnati, inda ya bayyana muhimmancin kare muhalli da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

 

Gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na tunkarar kalubalen muhalli da suka hada da sauyin yanayi da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

 

Gwamnati na aiki don samar da mafi tsabta, lafiya, kuma mafi dorewa yanayi ga dukan mazauna.

 

 

KHADIJAH ALIYU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: shara zubar da shara

এছাড়াও পড়ুন:

Aminu Ado ya soke hawan salla don gudun rikici a Kano

Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da bikin hawan salla bayan shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi.

Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a jihar, biyo bayan shiga ruɗani da jama’a suka yi.

Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4

Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga ruɗani a Kano saboda rikicin masarauta, biyo bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Tun farko, duka sarakunan biyu – Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin al’umma.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, Sarki Aminu, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan jin ra’ayin malamai da dattawa.

“Malamai da dattawa sun shawarce mu, kuma muna mutunta su. Don haka, bayan nazari tare da majalisar masarauta, mun yanke shawarar cewa mun janye domin zaman lafiya,” in ji shi.

Idan za a tuna, a makon da ya gabata ne, Aminu Ado, ya aike wa ’yan sanda takardar neman izinin gudanar da hawan salla, bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci Muhammadu Sanusi II, ya shirya yin hawan salla a bana.

Sarkin ya jaddada cewa bikin hawan salla ba abu ne da ya zama wajibi ba idan zai iya haddasa rikici da asarar rayuka.

“Idan akwai fargabar cewa hawan salla zai haddasa tashin hankali da asarar rayuka ko dukiyoyi, to, yana da kyau a daina,” in ji shi.

A gefe guda, al’ummar Kano sun nuna damuwa kan yadda rikicin masarautar ke ci gaba da yin tasiri a rayuwarsu.

Ana sa ran wannan matakin zai rage fargabar da ake ciki, tare da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’an Tsaro A Jihar Kano Na Tarayyar Najeriya Sun Hana Bikin Dabar NA Sallar Bana
  • Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki
  • An Fitar Da “Takardar Ci Gaban Sha’anin Hakkin Dan Adam A Xizang A Sabon Zamani”
  • ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
  • Gwamnatin Amurka Tana Shirin Dakatar Da Bada Kudaden Tallafi Don Samar Da Wasu Magunguna
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Hana Baƙin Haure Shigowa Nijeriya Ba Bisa Ƙa’ida Ba
  • Sallah: ’Yansanda Sun Yi Alƙawarin Tabbatar Da Tsaro A Kano
  • Za a Fara Cin Moriyar Shirin BEAR III Na UNESCO da Koria Ta Kudu Jihar Kano
  • Aminu Ado Ya Soke Hawan Sallah Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Kano
  • Aminu Ado ya soke hawan salla don gudun rikici a Kano