Gwamnatin Kwara Ta Kaddamar Da Kwas Ga Dalibai Makarantun 50
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da shirin horas da makarantun firamare da kananan makarantun gwamnati 50 a fadin jihar domin su iya amfani da fasahar ziyyana shafin internet.
Da yake gabatar da shirin a madadin Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq a Makarantar Sakandare ta Bishop’s Smith Junior Ilorin, babban mai ba gwamna shawara na musamman, Alhaji Sa’adu Salau, ya ce shirin na dijital ya kasance don ƙarfafa fannin ilimi.
A cewarsa shirin ya shafi sama da dalibai 150 a kowace makarantu 50 na gwamnati a matakin gwaji.
Ya ce idan aka kafa harsashin tsarin zamani, yaran jihar Kwara ba za su koma baya a tsakanin takwarorinsu na duniya ba.”
Gwamna AbdulRazaq yace sauran makarantun gwamnati da za su ci gajiyar wannan karimcin a babban birnin kasar sun hada da makarantar Sarauniya Elizabeth, Makarantar Grammar Ilorin, da kuma makarantar firamare ta Sheikh Alimi.
A nasa bangaren, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kwara kan harkokin dijital da kirkire-kirkire, Ishola Kayode, ya ce manufar shirin shi ne tabbatar da cewa daliban makarantun gwamnati ba su koma baya ba a duniyar dijital.
Ya ce daliban za su zama masu ilimin zamani, inda ya ce za su iya magance matsalolin da ke addabar al’ummarsu.
Ya ce za a fadada shirin bayan tantance bayanan da aka yi.
A nata jawabin shugabar makarantar Bishop’s Smith College (Junior Session), Mrs Akanbi Janet Ayoola, ta ce aikin na daya daga cikin mafi kyawun shawarar da gwamnatin jihar ta dauka a zamanin da fasahar sadarwa da fasahar kere-kere suka zama abin bukata na rayuwa.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin jihar Kano ta hana zubar da shara a Titin Kotu
A kokarin da take yi na magance kalubalen muhalli da inganta ayyukan sarrafa sharar gida mai dorewa, gwamnatin jihar ta hana zubar da shara a filin titin kotu.
Wannan shawarar na da nufin hana yaduwar cututtuka da kuma kare lafiya da amincin mazauna da masu wucewa.
A yayin ziyarar da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya kai wurin ya bayyana damuwarsa kan illar muhalli da kiwon lafiya daga zubar da shara.
Ya jaddada kudirin gwamnati na samar da ingantattun dabarun sarrafa shara don kare lafiyar jama’a da muhalli.
Dokta Hashim ya ba da umarnin kwashe sharar da suka taru a yankin, sannan ya shawarci mazauna yankin da su rika zubar da sharar su a wurin da aka kebe a garin Sallari.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga kokarin gwamnati, inda ya bayyana muhimmancin kare muhalli da kuma samar da ci gaba mai dorewa.
Gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na tunkarar kalubalen muhalli da suka hada da sauyin yanayi da kuma samar da ci gaba mai dorewa.
Gwamnati na aiki don samar da mafi tsabta, lafiya, kuma mafi dorewa yanayi ga dukan mazauna.
KHADIJAH ALIYU