Nan Ba Da Jimawa Ba Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ƙirar Nijeriya Zai Fara Tashi – NASENI
Published: 27th, February 2025 GMT
Hukumar bunƙasa ƙere-ƙere ta ƙasa (NASENI) ta bayyana cewa an kusa kammala aikin ƙera jirgin sama mai saukar ungulu na farko da aka yi a Nijeriya, kuma nan ba da jimawa ba za a fara gwajin tashinsa. Wannan ci gaba na daga cikin yunƙurin ƙasar wajen bunƙasa fasahar masana’antu da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Manajan Ayyuka na Cibiyar Bunƙasa Jiragen Sama ta NASENI, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa aikin yana kan hanya, inda ake amfani da dabaru na zamani don haɗa jirgin saman mai suna “Nigerian Chopper.” Ya ce hukumar ba wai tana ƙirƙiro wata sabuwar fasaha ba ne, sai dai tana inganta shirye-shiryen da aka fara tun farko, wanda ya haɗa da jirgin sama mai saukar ungulu da kuma jiragen sama marasa matuƙi (UAVs).
Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima… NASENI Ta Dukufa Kere-kere Domin Kawo Saukin Rayuwa A Nijeriya –KhalilInjiniya Kareem ya bayyana cewa hukumar ta samo wasu sassa na jirgin sama daga ƙasashen da suka ci gaba a tsarin “Semi Knock Down” (SKD) da “Complete Knock Down” (CKD), tare da amfani da ilimin kimiyya da injiniyanci wajen haɗa su da inganta su. Ya jaddada cewa NASENI tana da himma wajen bunƙasa fasahar cikin gida domin rage dogaro da ƙasashen waje da kuma ƙarfafa masana’antu a ƙasar.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwajin tashin jirgin saman zai fara nan ba da daɗewa ba, yayin da ake kammala ƙarin cikakkun matakai na fasaha. Wannan aiki na daga cikin shirin gwamnati na ƙarfafa ƙere-ƙere da fasaha a Nijeriya don inganta harkokin sufurin sama na cikin gida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gobe take Sallah a Nijeriya — Sarkin Musulmi
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.
Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi.
Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.