Sarkin Moroko Ya Buƙaci Yan Kasar Kada Su Yi Layya A Bana
Published: 27th, February 2025 GMT
Sarkin Moroko, Mohammed na shida, ya buƙaci ƴan ƙasar su kaurace wa layya a bana wanda al’ummar Musulmi masu hali ke yanka dabobbi, musamman rago a matsayin nuna godiya ga Allah bisa rayawa da ni’imomin da ya yi wa bayinsa.Sarkin ya ce sanarwar tasa na da alaƙa da karancin raguna da ake fuskanta a ƙasar sakamakon fari.
A watan Yunin bana ake sa ran gudanar da bikin sallar Layya. Layya ibada ce da al’ummar musulmi ke yi a cikin watan Zhul Hajji.
A bikin Sallar layyar ana yanka dabobbi da suka danganci raguna da awaki ta hanyar zubar da jini a kuma raba naman a matsayn kyauta da sadaka don neman kusanci ga ubanjigi.
Sai dai Sarki Mohammed na moroko ya umarci al’ummarsa su jingine batun layya a bana saboda fari ya haifar da karancin dabobbi a kasar.An samu raguwar raguna da kashi 40 cikin 100 a cikin shekaru 10 a ƙasar saboda fari.
Farashin nama yayi tashin gwaran zabi, kuma a kullum ake shigo da dubban raguna kasar daga Australia
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Trump Ya Yi Koyi Da Nixon
Ranar 21 ga watan Fabrairu ne aka cika shekaru 53 da shugaban kasar Amurka na lokacin Richard Nixon ya kawo ziyara kasar Sin a shekara ta 1972, ziyarar ta sauya tarihin duniya, ta kuma samar da tushen ci gaban yankin Asiya da tekun Pasifik cikin lumana. Lokacin da tunanin yakin cacar baka ya yi kamari a Amurka, Nixon ya fahimci muhimmancin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a ci gaban Asiya da duniya baki daya. Nixon, ya kasance dan siyasa mai ra’ayin mazan jiya wanda ya girma cikin yakin cacar baka, amma duk da haka ya keta shingayen mulkin mallaka, danniya da babakere na wancan lokaci don fahimta da sauke alhakin da ke kansa na tarihi, ta hanyar hadin gwiwa da tuntuba, wanda ya dace shugaban Amurka mai ci Donald Trump ya yi koyi daga gare shi. Sai dai shi Trump ya zabi barazana da sa-in-sa a matsayin hanyar sadarwarsa. Karin harajin kashi 25 kan karafa da goron ruwa da Trump ya yi barazana, da karin harajin kashi 10 da ya dorawa kayayyakin kasar Sin, mataki ne da ya yi watsi da ruhin dangantaka da Nixon ya shimfida, ya kuma karya lagon alakar Amurka da Sin. Bugu da kari, da dama daga cikin sanannun “masu adawa da kasar Sin” sun samu gindin zama a gwamnatin Trump.
Duk da cewa, akwai da yawa daga cikin kalaman Trump dake nuna yakininsa na cewa zai iya “sassantawa” da kasar Sin da kuma yabon da yake yi wa shugaban kasar Sin Xi Jinping, za a iya samun wata boyayyar ajanda karkashin manufar Trump fiye da kallon kasar Sin a matsayin “kishiya ko abokiyar takara”. To, idan duk harajin da ya yi barazanar kakabawa suka fara aiki, ba shakka matakin zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, amma zai fi yin tasiri ga mabukatan Amurka. Wasu na ganin zai iya haifar da koma bayan tattalin arziki a duniya. Kana, zai yi matukar wahala a kai ga cimma matsaya da fahimtar juna wajen tunkarar dabaru ko wasu batutuwa masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu idan har aka fara gasar daukar matakan da za su illata tattalin arziki. Gaskiyar lamarin ita ce, farfado da tattalin arzikin Amurka kamar yadda Trump ya yi ikirari na bukatar karin zuba jari a ababen more rayuwa na Amurka da kuma kokarin hadin gwiwa daga bangaren gwamnatin Amurka don habaka fannin kimiyya da fasaha, sai dai kash, babu dayan wadannan da ke faruwa a halin yanzu. Maslaha mafi sauri da sauki ita ce yin aiki da kasar Sin kamar yadda Nixon ya yi, ba yin adawa da ita ba. Amma fa da Trump zai gane. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp