Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan
Published: 27th, February 2025 GMT
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025.
Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labara.
Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Ramadan ya sanar da hakimi ko uban ƙasar da ke kusa da shi.
Daga nan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.
Ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da suke yi na addini.
Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, kuma al’ummar Musulmi na azumtar sa baki ɗaya.
Azumin Ramadan shi ne ka uku a cikin ginshikan addinin Musulunci guda biyar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Azumin Ramadan Ramadan Sarkin Musulmi Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu
Kotun Majistire da ke zama a Sabo a unguwar Yaba ta Jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad.
Mai Shari’a Ejiro Kubenje, wanda ya karanta hukuncin ya ce babu wata ayar tambaya kan mutanen biyu game da rasuwar Mohbad.
Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin KongoHaka nan ma kotun ta sallami Oodunni Ibrahim, wanda ake kira Primeboy da tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde.
Sai dai hukuncin ya ce za a gurfanar da ma’aikaciyar jinyar da ta kula da Mohbad gabanin mutuwarsa, wato Feyisayo Ogedengbe, da ɗaya daga cikin abokan marigayin, Ayobami Sadiq bisa tuhumar su da sakaci, wanda ya kai ga mutuwar matashin mawaƙin.
Ana iya tuna cewa, mutuwar Mohbad a shekarar 2023 dai ta janyo ce-ce-ku-ce matuƙa musamman a kafafen sada zumunta na zamani a ciki da wajen Nijeriya.
Kazalika, a wancan lokacin an gudanar da zanga-zanga a jihohin Legas da Oyo da Delta, don neman a binciki musabbabin mutuwar ta shi.