Aminiya:
2025-02-27@15:28:09 GMT

An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS

Published: 27th, February 2025 GMT

Damfarar da aka yi wa mutane ta hanyar tura kuɗi ta banki ya ninku sau uku zuwa Naira biliyan 52 a Najeriya.

Alƙaluma ‘n Hukumar Kula da Tsarin Tura Kuɗi Tsakanin Bankuna (NIBSS) ya nuna a shekara huɗu da suka gabata aka samu wannan karin daga Naira biliyan 11 zuwa biliyan 52,

Alƙaluman sun nuna a shekara shekarar 2024 an yi asarar Naira biliyan 52, kusan ninki biyar na Naira biliyan 11,2 da aka yi asara a shekarar 2020.

Rahoton na NIBSS ya bayyana cewa masu damfarar sun yi yunƙurin sace Naira biliyan 86.4 a shekarar 2024.

 

The figure is coming on the heels of the latest GDP figures released by the National Bureau of Statistics showing a fourth quarter 2024 growth of 3.8 percent, the fastest in three years, driven by the services sector, including finance and insurance.

“Satar da ’yan damfara suka yi wa mutane ta hanyar hadahadar kuɗi ta zamani ta ƙaru saidai a cikin shekaru biyar da suka gabata,” in ji rahoton na NIBSS.

Ya ci gaba da cewa, “’yan damfarar na amfani da dabaru iri-iri, ciki har da amfani da bayanan tsofaffi ko ƙananan yara ko ’yan ƙasashen waje ko kuma a bayanan mutane ba da saninsu ba, wajen buɗe asusun banki.

“An gano yadda aka sace Naira miliyan 400 ta hanyar amfani da asusun da aka buɗe da bayanan mutane ba da saninsu ba ko kuma tsofaffi,” in ji rahoton.

Ya bayyana cewa an yi nasarar ƙwato wasu daga cikin kuɗaɗen sannan ana b’cingabda bincikar jami’an bankin da ake zargin hannunsu a badaƙalar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Damfara tura kuɗi ta banki Naira biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka Ta Laftawa Iran Wasu Sabbin Takunkumai

Gwamnatin Trump ta saka sabbin takunkumai kan wasu mutane da ke da alaka da wani kamfanin fitar da mai na Iran.

Takunkuman sun shafi mutane 22 da jiragen ruwa 13 da ke da alaka da masana’antar mai ta Iran.

Wadannan takunkumin wani bangare ne na matsin lamba na shugaban Amurka Donald Trump kan Iran.

Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka ta sanar da cewa, takunkumin na da nufin gurgunta harkokin hada-hadar kudi da kuma cinikin man fetur na Iran, da nufin takaita shirinta na nukiliya.

Iran dai na mai kakkausar suka kan takunkuman na Amurka, tana mai kallonsu a matsayin sabawa ka’idojin kasa da kasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno
  • Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90% a jihar
  • Gwamnatin Jigawa Ta Biya  Sama Da Naira Miliyan 730 Ga Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Katsina Ta Ƙaddamar Da Shirin Tallafin Abinci Na Naira Biliyan 4
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Sama Da Naira Biliyan 5 Ga Wadanda Aikin Tituna Ya Shafa
  • Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS
  • Mutum 7,000 Suka Mutu A Rikicin Gabashin Kwango Tun Daga Watan Janairu
  • Amurka Ta Laftawa Iran Wasu Sabbin Takunkumai
  • Kasar Sin Ta Cimma Burin Magance Gurbatar Yanayi A Shekara Ta 2024