An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sanda
Published: 27th, February 2025 GMT
An shiga ruɗani bayan Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya koma majalisar tare da rakiyar ’yan sanda.
An sauke Obasa daga muƙaminsa a ranar 13 ga watan Janairu kan zargin yin amfani da ofis ɗinsa ba daidai ba.
An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a AdamawaAn maye gurbinsa da Mojisola Meranda, wanda hakan ya haifar da rarrabuwar kai a majalisar da kuma jam’iyyar APC mai mulki a Jihar.
Rahotanni sun nuna cewa an matsa wa Meranda da ta sauka daga muƙaminta, bayan da ake zargin cewa Shugaba Bola Tinubu bai gamsu da sauke Obasa daga muƙaminsa ba.
A safiyar ranar Alhamis, labari ya bayyana cewa an janye wa Meranda jami’an tsaron da ke ba ta kariya.
A gefe guda guma an mayar wa jami’an da za su ba shi kariya, alamar da ke nuna ana shirin dawo da shi kan muƙaminsa.
Wata majiya ya shaida wa Aminiya cewa Obasa ya shiga zauren majalisa tare da ’yan sanda, yana ƙoƙarin shiga ofishin kakakin majalisar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jami an Tsaro Majalisar Dokoki Ruɗani
এছাড়াও পড়ুন:
UEFA: Wasan Arsenal Da Real Madrid Ya Haddasa Rikici A Tsakanin Magoya Bayan Kungiyoyin A Kano
An tabbatar da cewa, tashin hankalin ya barke ne jim kadan bayan da alkalin wasa ya busa tashi daga wasan, kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto a safiyar ranar Alhamis, kuma kawo yanzu babu tabbacin ko an samu raunika a yayin rikicin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp