Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar.
A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci.
Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan ɗaya da muhimman kayayyakin amfanin gona kamar irin su iri, taki, famfunan ban-ruwa, maganin ƙwari da magungunan kashe ciyawa.
“Wannan dabarar ba kawai za ta inganta dogaro da kai ba ce har ma da rage kashe kuɗaɗen gwamnati,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, rabon kayan tallafin zai taƙaita ne ga ƙananan hukumomin jihar guda biyu kawai daga cikin 27 a shekarar 2025 saboda ƙalubalen da suke fuskanta.
“Ƙananan Hukumomin da za su sami tallafin abinci a shekara mai zuwa su ne: Ngala da Kala-Balge saboda yanayi na musamman.
“Waɗannan yankuna sun fuskanci mummunar ɓarna a gonakinsu daga giwaye kuma sun fuskanci ambaliyar ruwa. Don haka, a shekarar 2025, gwamnatin Jihar Borno za ta samar da kayayyakin tallafin abinci ga Ngala da Kala-Balge kaɗai,” inji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Umara Zulum Umara
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Iran Sun Kammala Atisayen Zulfikar 1403 Da Faretin Sojojin Ruwa
Sojojin kasar Iran sun kammala atisayen hadin giuwa mai suna Zolfaghar 1403 a jiya Talata tare da faretin sojojin Ruwa na kasar.
Atisayen ya hada sojojin sama da na ruwa ne, saboda jarraba yadda bangarorin biyu zasu yi aiki tare a lokacin yaki, duk da cewa ko wani bangare yana aiki a inda ya kore, ya ke kuma da masaniya a kansa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin zasu hada kai don tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu cikin ruwa da kan tudu tare.
Manya-manyan kwamandojin sojojin kasar wadanda suka hada da Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin babban kwamnadan sojojin kasar a bangaren tsare-tsare. Da kuma Manjo Janar Abdulrahim Musavi babban kwamandan sojojin kasar iran.
Atisayen ya hada rawar daji a karkashin ruwa don gwada aiki da makamai, da kuma tudun ruwa shi ma don gwada makaman da ake da su. Sannan da yadda za’a yi rundunonin su yi aiki tare, idan bukatar haka ta taso.