Abba ya ba da umarnin bincike kan rage wa ma’aikatan Kano albashi
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan ƙorafe-ƙorafen datse wa ma’aikatan jihar albashi.
Hakazalika ya ce a yi bincike kan rashin biyan wasu ma’aikatan albashinsu.
Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sandaYa bayyana lamarin a matsayin cin zarafin ma’aikata da tauye musu haƙƙi.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ma’aikatan sun shafe watanni ba tare da karɓar cikakken albashinsu ba.
Gwamna Abba ya sha alwashin gano waɗanda ke da hannu a lamarin tare da hukunta su.
“Wannan gwamnati ba za ta amince da zaluntar ma’aikata ba.
“Duk wanda aka samu da hannu a wannan laifi zai fuskanci hukunci,” in ji shi.
Don shawo kan matsalar, gwamnan ya kafa kwamitin bincike mai mutum bakwai ƙarƙashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, Kwamishinan Kula da Ci Gaban Karkara wanda kuma shi ne tsohon Akanta-Janar na Jihar.
Akwai ƙwararru a harkar kuɗi da manyan jami’an gwamnati a cikin kwamitin, waɗanda za su duba takardun albashi daga watan Oktoban 2024 zuwa Fabrairun 2025.
Ayyukan kwamitin sun haɗa da gano ma’aikatan da abin ya shafa, tantance asarar kuɗi da kuma bayar da shawarwari kan yadda za a magance matsalar gaba ɗaya.
Gwamnan ya bai wa kwamitin wa’adin kwana bakwai don kammala bincikensa da kuma miƙa rahoton.
Gwamna Abba ya tabbatar wa ma’aikatan jihar cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da adalci da kuma biyan albashi a kan lokaci a nan gaba.
Ya gargaɗi duk wanda aka samu da laifin yin almundahana da albashin ma’aikata cewa ba za a kyale shi ba.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne, ya ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnan.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Na Shirin Rufe Ofisoshin Jakadancinta Kimani 30 A Duniya
Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta har kimani 30 a kasashen duniya, amma mafi yawansu a kasashen Afirka.
Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurkan na fadar cewa gwamnatin shugaban Trump tana son ta rage yawan kashe kudade a ma’aikatar don amfani da su a cikin gida.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin tana son rage kudaden da ma’aikatar take kashewa a kan ofisoshin jakadunsu da kasha 50% da kuma rage tallafin da take bawa wasu kungiyoyi a wadan nan kasashe har da kasha 75%.
Labarin ya kara da cewa kasashen da shirin ya shafa dai akwai Lesotho, Eritrea, Afrika ta tsakiya, Congo Brazavile, Gambia, Sudan ta kudu,. Banda wadannan za’a rufe kananan ofisoshin jakadanci da ke birnin Durban na Afrika ta kudu, da kuma na Douala, da ke kasar Cameroon. Labarin yace ayyukan wadannan ofisoshin jakadanci zasu kuma ga kasashe makobta.
A kasahen turai da Asiya kuma Amurka zata rufe ofisoshin jakadancinta a tsibirin Malta, Luxembourg, da kuma wasu kananan ofisoshin jakadancin kasar a tarayyar Turai da Asiya.