Bankin Raya Afirka ( AFDB) Ya Bayyana Kasashen Da Tattalin Arzikinsu Yake Bunkasa Da Sauri A Cikin Nahiyar
Published: 27th, February 2025 GMT
Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da yin hashashen cewa gabashin Afirka zai zama sama da sauran yankunan nahiyar a cigaba.
Ana hasashen cewa a cikin rabin kasashen nahiyar za a sami habakar jumillar kudaden shiga ( GDP) daga 4.
A cikin yankin yammacin Afirka kuwa, an tsinkayo cewa tattalin arzikinsu zai tashi daga 4.1% a 2024,zuwa 4.6% a 2025, kuma kasashe irin su Togo, Benin, Cote De Voire, da Gambiya za su sami bunkasa mai karfi.
A Arewacin Afirka kuwa jumillar kudaden shiga ( GDP) zai tashi daga 2.7% a 2024, zuwa 4.2 a 2026.
Kasar Sudan Ta Kudu ce ake hashshen cewa za ta zama zakara a fadin nahiyar ta Afirka wajen bunkasar jumillar kudaden shiga da kaso 34.4%,saboda sake dawowar hako man fetur da kuma fitar da shi zuwa kasuwannin duniya.
Ita kuma Senegal tattalin arzikin nata zai bunkasa ne da kaso 8.9% saboda man fetur, iskar Gas, muhimman cibiyoyi da kuma noma da kiwo.
Kasashen jamhuriyar Nijar, Djibouti, Togo Habasha da Benin da Coye De Voire za su samun bunkasa da kaso 6.3.6.9.% saboda zuba hannun jari a cibiyoyi masu muhimmani da gina su.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Moroko Ya Buƙaci Yan Kasar Kada Su Yi Layya A Bana
Sarkin Moroko, Mohammed na shida, ya buƙaci ƴan ƙasar su kaurace wa layya a bana wanda al’ummar Musulmi masu hali ke yanka dabobbi, musamman rago a matsayin nuna godiya ga Allah bisa rayawa da ni’imomin da ya yi wa bayinsa.Sarkin ya ce sanarwar tasa na da alaƙa da karancin raguna da ake fuskanta a ƙasar sakamakon fari.
A watan Yunin bana ake sa ran gudanar da bikin sallar Layya. Layya ibada ce da al’ummar musulmi ke yi a cikin watan Zhul Hajji.
A bikin Sallar layyar ana yanka dabobbi da suka danganci raguna da awaki ta hanyar zubar da jini a kuma raba naman a matsayn kyauta da sadaka don neman kusanci ga ubanjigi.
Sai dai Sarki Mohammed na moroko ya umarci al’ummarsa su jingine batun layya a bana saboda fari ya haifar da karancin dabobbi a kasar.An samu raguwar raguna da kashi 40 cikin 100 a cikin shekaru 10 a ƙasar saboda fari.
Farashin nama yayi tashin gwaran zabi, kuma a kullum ake shigo da dubban raguna kasar daga Australia