Iran Za Ta Rubanya Samar Da Wutar Lantarki Ta Makamashin Nukiliya Har Sau Uku Zuwa 2029
Published: 27th, February 2025 GMT
Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu.
Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa:
“ Za mu kara yawan wutar lantarkin da muke samarwa da megawati 2000 a kowace sa’a daya daga nan zuwa karshen zangon na bakwai na tsare-tsaren ci gaba da ake yi a kowace shekara 5.
Salami ya ce za a kara megawati 1,000 a cikin kowace sa’a da hakan zai mayar da abinda ake samarwa zuwa megawati 3,000 a cikin kowace sa’a.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
A Kalla Mutane 9 Ne Su Ka Yi Shahada A Gaza
HKI tana ci gaba da kai wa yankunan Gaza mabanbanta hare-hare da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai a yau Laraba.
Tun da safiyar yau Laraba ne HKI ta kai hari akan wani gida dake unguwar “al-Tuffah” dake cikin birnin Gaza da hakan ya sa mutane 6 su ka yi shahada.
A yankin Jabaliya kuwa jiragen yakin HKI sun kai hari akan wani gida da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3.
A wani labarin kungiyar ” Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba” ta bayyana cewa; Isra’ila ta mayar da yankin Gaza zuwa Makabarta.
Kungiyar ta bayyana cewa; Yadda Isra’ila take fadada wuraren da take kai wa hare-hare ta sama, kasa da ruwa a yankin Gaza , tana korar mazauna yankin ta hanyar amfani da karfi da kuma hana shigar da kayan agaji zuwa yankin.
Kungiyar ta kara da cewa; Abinda Isra’ilan take yi ya sa rayuwa ta yi tsanani a cikin yankin da kuma mayar da shi zuwa babbar makabarta.
Jami’a mai kula da ayyukan kungiyar a Gaza, Amandi Barirol ya bayyana cewa; A halin yanzu Falasinawa ba su da wanda zai taimaka musu.”