Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki
Published: 27th, February 2025 GMT
Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato, sun fara yajin aiki a karon farko tun bayan kafuwar jami’ar sama da shekaru 12 da suka gabata.
A wata sanarwa da shugabansu, Saidu Isah Abubakar, tare da Sakataren Jami’ar, Hassan Aliyu, suka fitar, sun bayyana cewa an yanke shawarar shiga yajin aikin ne a ranar Laraba.
“Dukkanin harkokin karatu, karantarwa, jarabawa, duba ɗalibai da makin jarabawa sun tsaya har sai an cimma matsaya,” in ji sanarwar.
Malaman sun ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tilasta wa gwamnatin jihar, biyan buƙatun da suka jima suna gabatarwa.
Sanarwar, ta ce ba su gamsu da yadda gwamnati da majalisar gudanarwar Jami’ar ke tafiyar da al’amuran da suka shafi ci gaban Jami’ar ba.
Saboda haka, a taron da suka gudanar, mambobin ƙungiyar sun amince da fara yajin aiki daga ranar 26 ga watan Fabrairu, 2025.
Ƙungiyar ta ce ta kafa kwamitin da zai tabbatar da an bi umarnin yajin aikin a Jami’ar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara, ta tura jami’ai 415 a fadin jihar domin tabbatar da tsaro a duk lokacin bukukuwan Easter.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar, ASCII Umar Mohammad M. ya fitar, ya ce jami’an sun jibge a wuraren ibada daban-daban da sauran muhimman wurare a fadin kananan hukumomi 14 na jihar domin tabbatar da tsaro da kuma gudanar da bukukuwan lafiya.
A cewar sanarwar, kwamandan jihar, Sani Mustapha, ya jaddada kudirin hukumar NSCDC karkashin jagorancin kwamandan Janar, Dakta Ahmed Abubakar Audi, na magance matsalolin tsaro a fadin kasar nan.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar a jihar Zamfara ta shirya tsaf domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata tare da bayar da gudumawa wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.
REL/AMINU DALHATU