Kwanan baya, kwamitin kula da aikin lantarki na duniya (IEC) ya gabatar da ka’idar sarrafa mutum-mutumin inji mai kula da tsoffi. Ka’idar da kasar Sin ta ba da jagorancin tsarawa, ta tabbatar da yadda za a tsara da sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi bisa halayen da tsoffi suke ciki, ta kuma tabbatar da yadda za a gudanar da bincike kan mutum-mutumin inji, yayin ba da izini gare su.

Lamarin da ya ba da tabbaci ga bunkasuwar aikin sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi yadda ya kamata.

Bayanin ya nuna cewa, an tsara ka’idar bisa bukatun tsoffi a fannonin samun kulawa cikin harkokin yau da kullum, da kiwon lafiya da dai sauransu. Haka kuma, ana fatan tsara mutum-mutumin inji bisa mabambanta bukatu, ban da ingancinsu, da tsimin makamashi, ana kuma fatan za su iya sa ido kan lafiyar jiki, da gudanar da harkokin gaggawa yadda ya kamata, tare da tuntubar iyalan tsoffi da masu ba da jinya cikin lokaci da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [21]

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [19]

Fashin Baƙi:

Maganar da Ibn Juzai ya fadi a kan tawakkali tana bayyana ainihin ma’anar dogaro ga Allah cikin dukkan al’amura na rayuwa, wato samun alheri, da kiyaye shi, da kuma kauce wa masifa, ko kuma fita daga cikin masifa idan ta afku. Tawakkali yana nufin dogaro ga Allah da zuciya ɗaya tare da yin ƙoƙari da dalilan da Allah ya tanadar don cimma buri. Ba wai kawai mutum ya jingina da Allah ba tare da yin aiki ba, ko kuma ya dogara da aikinsa ba tare da tawakkali ba, sai dai a haɗa su duka.

Bangarorin Tawakkali:
Ibnu Juzai ya kasa tawakkali zuwa manyan bangarori guda biyu:
● Tawakkali wajen samun alheri ko kiyaye shi. Mutum ya riƙa dogara da Allah wajen samun ni’ima kamar arziki, da lafiya, da ilimi, da duk wani alheri.Idan mutum ya sami alheri, to yana buƙatar tawakkali don kiyaye shi, saboda shi kansa alheri yana buƙatar kulawa da albarka daga Allah.
● Tawakkali wajen kawar da masifa ko saukinta bayan ta afku. Idan mutum yana fuskantar wata musiba kamar talauci, ko rashin lafiya, ko wata matsala, zai dogara ga Allah don samun sauki. Idan masifa ta riga ta faru, mutum yana tawakkali wajen samun mafita da sauƙin abin da ya same shi a wurin Allah.

A Musulunci, tawakkali ba yana nufin mutum ya zauna ba tare da yin aiki ba. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Da kun yi tawakkali ga Allah da gaske, da ya ciyar da ku kamar yadda yake ciyar da tsuntsaye. Suna fita da sassafe cikinsu da yunwa, kuma suna dawowa da yamma cikinsu a ƙoshe.” Hadisi ne ingantacce Tirmizi da Ɗabarãni ne suka ruwaito.

Wannan hadisi yana nuna cewa tsuntsaye ba sa zama kawai suna jiran Allah ya ciyar da su, sai dai suna aiki ta hanyar sammako neman abincinsu a wurin Allah. Haka ma mutum yana tawakkali ga Allah amma yana yin kokari da aiki tuƙuro da dogaro ga Allah domin kaiwa ga gaci.

Tawakkali yana daga cikin manyan siffofin muminai kamar yadda Allah Ya ce a cikin Alkur’ani: “Kuma ga Allah kaɗai za ku dogara, idan kun kasance ku mummunai ne” Suratul Mã’idati aya ta 23.

Fa’idojin Tawakkali:

Fa’idodin tawakkali sun haɗa da:
• Samun kwanciyar hankali da nutsuwa.
• Rage damuwa da fargaba.
• Samun kariya daga Allah.
• Samun albarka da nasara a rayuwa.

Bambancin Tawakkali da Riƙon Hannu (Tawãkul):
Akwai bambanci tsakanin tawakkali da tawaakul: Domin tawakkali yana nufin dogaro ga Allah tare da yin aiki. Shi kuma tawãkul k yana nufin nuna jingina ga Allah ba tare da bin tsarin da Allah Ya shimfiɗa na riskar abubuwa ba.

A taƙaice, Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, yana nuni da cewa tawakkali yana rufe dukkan fannoni na rayuwar mutum wajen neman alheri da kiyaye shi, har zuwa kauce wa masifa da fita daga gare ta. Tawakkali yana buƙatar cikakken imani da Allah tare da bin hanyoyin da suka dace da Allah Ya tsara na samun abubuwan rayuwa. Wannan shi ne ainihin fahimtar tawakkali a Musulunci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar
  • Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo
  • An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Filato
  • An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [21]
  • Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand
  • ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH
  • Yadda Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi
  • Cutar sanƙarau ta yi ajalin mutum 3 a Gombe
  • ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano