Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa
Published: 27th, February 2025 GMT
Wasu gungun ‘yan Boko Haram ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki cikin dare a garin Kwapre da ƙauyukan da ke gundumar New Yadul a ƙaramar hukumar Hong a Jihar Adamawa.
Harin wanda ya fara daga misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, kuma ya ɓarnata dukiyoyi a tsakiyar daren.
Al’ummar yankin sun ce, an ƙona wuraren ibada da makarantu da gidaje da wuraren kasuwanci, sannan an wawushe dukiyoyi na miliyoyin Naira.
Mista Joel Kulaha, Hakimin garin Kwapre da Abalis Jawaja, kuma dagacin ƙauyen, ya ce maharan sun farwa al’ummar garin, inda suka ƙona gine-gine tare da kwashe kayayyaki masu daraja.
Sun ce, an yi sa’a ba a rasa rayuka a harin ba, domin mazauna yankin sun yi gargaɗin ƙaruwar barazanar harin, sun tsere daga gidajensu kafin maharan su iso.
“Mun tsere da rayukanmu, amma duk abin da muka mallaka ya tafi,” kamar yadda Kulaha ya koka, yana kwatanta harin da aka kai.
An samu rahoton cewa dakarun sojin da ke kusa da Garaha sun mayar da martani kan harin da sanyin safiya, inda suka fatattaki maharan.
Sai dai mazauna yankin sun ce matakin sojan ya makara ne domin daƙile ɓarnar da ta ɓarke ƙauyukan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamawa Boko Haram Kwapre Hong
এছাড়াও পড়ুন:
Sallah: Hadimin gwamnan Sakkwato ya bai wa magoya bayan APC kyautar N22m
Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar.
Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, da Gwamna Ahmad Aliyu, bisa damar da suka ba shi don ba da gudunmawarsa ga ci gaban jihar.
An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu“Wannan tallafi saƙon godiya ne daga shugabanninmu zuwa gare ku. Idan ba su ba mu dama ba, ba za mu iya wannan ba.
“Kuma muna shirye mu ƙara tallafawa a duk lokacin da buƙata hakan ta taso,” in ji shi.
Ya jinjina wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Arewa, bisa sadaukarwar da suka yi wajen ganin jam’iyyar APC ta yi nasara, inda ya ce hakan ne ya sa suka cancantar a yi masu hidima.
Bajare, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa magoya bayan jam’iyyar lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ci gaban tafiyar siyasarsu.
Dangane da tsarin rabon tallafin, ya ce kowane mutum da aka zaɓa zai amfana da kuɗi tsakanin Naira 100,000 zuwa miliyan ɗaya, ya danganta da matsayinsa.
Haka kuma ya yi fatan al’umma za su gudanar da shagalin sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.