Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero daga fadar Nassarawa
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗauki mataki na cire Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, daga Fadar Nassarawa, wanda ta ce zamansa na haddasa tashin hankali a jihar.
Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, ya yi wannan kira.
Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kazaYa bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Fadar Gwamnatin Kano yayin rabon kayan tallafi da ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tarauni, Hon.
Ya zargi wasu mutane na amfani da zaman Aminu Ado a fadar Nasarawa don cimma muradun kansu da kuma haddasa rikici a Kano.
“Muna kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya cire Sarkin da ya naɗa ya kuma ajiye shi a maƙabarta,” in ji Gwarzo.
“Mutanen Kano, musamman matasa, sun gaji da wannan abun kunya.
“Abun mamaki ne a ce a dimokuraɗiyya ana tura jami’an tsaro suna harba wa masu zanga-zangar lumana barkonon tsohuwa, wasu rahotanni ma suna cewa an yi amfani da harsasai na gaske.
“Da yamma, motocin sojoji sun yi sintiri a cikin gari, har ma sun tsaya a kofar gidana. Amma muna so mu bayyana cewa ba za a razana mu ba.
“Wannan dimokuraɗiyya ce, kuma dole ne a mutunta ta, ko ana so ko ba a so. Muna goyon bayan matasan da suka fito domin bayyana damuwarsu.
“Shugaban ƙasa ya ɗauke Sarkin da ya naɗa, ya kai shi jiharsa. Kano tuni tana da Sarki, kuma wannan Sarki shi ne Muhammadu Sanusi II,” in ji shi.
“A yau, ko kai waye, ko da kai ne ‘Sarkin Duniya,’ ba za ka iya naɗa Sarki a Kano ba sai dai idan kai ne Gwamna Abba Kabir Yusuf.”
Gwarzo ya jaddada cewar zaman Aminu Ado a fadar Nasarawa wata maƙarƙashiya ce don hana gwamnatin jihar gudanar da mulki yadda ya kamata.
Ya kuma soki amfani yadda jami’an tsaro ke amfani da ƙarfi a kan masu zanga-zanga, inda ya ce ‘yancin yin zanga-zangar lumana haƙƙi ne a dimokuraɗiyya.
Ya bayyana cewa mutanen Kano suna da haƙƙin neman a cire Aminu Ado Bayero, kuma ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin wanzuwar zaman lafiya.
Gwamnatin Kano, ta kuma jaddada cewa doka ce ta tabbatar da naɗin tsohon sarki, kuma doka ce ta dawo da Muhammadu Sanusi II, wanda ta ce dole ne a mutunta doka kuma a bi ta yadda ya kamata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Ado Bayero Fadar Nassarawa gwamnati Jami an Tsaro Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo mataimakin gwamna sarki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin jihar Kano ta hana zubar da shara a Titin Kotu
A kokarin da take yi na magance kalubalen muhalli da inganta ayyukan sarrafa sharar gida mai dorewa, gwamnatin jihar ta hana zubar da shara a filin titin kotu.
Wannan shawarar na da nufin hana yaduwar cututtuka da kuma kare lafiya da amincin mazauna da masu wucewa.
A yayin ziyarar da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya kai wurin ya bayyana damuwarsa kan illar muhalli da kiwon lafiya daga zubar da shara.
Ya jaddada kudirin gwamnati na samar da ingantattun dabarun sarrafa shara don kare lafiyar jama’a da muhalli.
Dokta Hashim ya ba da umarnin kwashe sharar da suka taru a yankin, sannan ya shawarci mazauna yankin da su rika zubar da sharar su a wurin da aka kebe a garin Sallari.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga kokarin gwamnati, inda ya bayyana muhimmancin kare muhalli da kuma samar da ci gaba mai dorewa.
Gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na tunkarar kalubalen muhalli da suka hada da sauyin yanayi da kuma samar da ci gaba mai dorewa.
Gwamnati na aiki don samar da mafi tsabta, lafiya, kuma mafi dorewa yanayi ga dukan mazauna.
KHADIJAH ALIYU