Leadership News Hausa:
2025-02-28@02:39:03 GMT

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe

Published: 27th, February 2025 GMT

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe

Ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta janye binciken sashe na 232 kan shigo da jan karfe kasarta, inda ta bayyana cewa, zargin da ake yi na cewa kasar Sin na amfani da tallafin gwamnati da karfin samar da hajoji fiye da kima don gurgunta abokan takara kwata-kwata ba ya da tushe.

Kakakin ma’aikatar He Yadong ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a lokacin da yake amsa tambaya kan matakin da Amurka ta dauka na kaddamar da binciken sashe na 232 kan jan karfe da aka shigar da su kasar daga kasashen waje.

Ya kara da cewa, binciken na Amurka wani aiki ne na kashin kai da kariyar cinikayya wanda ta yi bisa fakewa da “tsaron kasa”, kuma matakin zai kara yin illa ga tsarin cinikayyar bangarori daban daban da kuma kawo cikas ga daidaiton tsarin samarwa, da rarraba hajoji tsakanin sassan kasa da kasa.

Kakakin ya ce, idan Amurka ta nace kan sanya karin haraji da sauran matakan takaitawa, Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kiyaye hakkoki da moriyarta. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Ya Jaddada Cewa Dole Ne A Dauki Sabbin Nauyi Da Sabbin Ayyuka A Sabuwar Tafiya Ta Inganta Zamanintarwa Irin Ta Kasar Sin

Kwanan nan, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kuma sakatarorin sakatariyar hukumar, da mamban kungiyar JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, majalisar gudanarwa kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, da kuma darektan kwamitin JKS na kotun jama’a ta koli kuma hukumar gabatar da kararraki ta koli, sun ba da rahotannin tantance nasarorin aiki ga kwamitin kolin JKS da kuma babban sakatarensa Xi Jinping.

Xi ya duba rahotannin kuma ya gabatar da muhimman bukatu. Yana mai jaddada cewa, shekarar bana ita ce shekarar karshe ta shirin shekaru biyar-biyar na 14, kuma muhimmiyar shekara ce ta kara zurfafa yin gyare gyare. Dole ne a mai da hankali cikin natsuwa game da kalubalen da sauye-sauyen yanayi na cikin gida da na waje suka haifar, da tabbatar da ingantaccen ci gaba, da habaka bude kofa ga waje a babban mataki, da inganta rayuwar jama’a a kai a kai. Dole ne mu dauki sabbin nauyi kuma mu yi sabbin ayyuka a sabuwar tafiya ta inganta zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • MDD Ta Yi Gargadi Akan Tsanantar Yunwa A Kasar Sudan
  • Sin Za Ta Kara Matsa Kaimi Ga Raya Sha’anin Mata Na Duniya
  • Al’umma Sun Nuna Alhininsu Kan Takaddamar Akpabio Da Sanata Natasha
  • Wakilin Sin: Dole Ne A Aiwatar Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza
  • Xi Ya Jaddada Cewa Dole Ne A Dauki Sabbin Nauyi Da Sabbin Ayyuka A Sabuwar Tafiya Ta Inganta Zamanintarwa Irin Ta Kasar Sin
  • Shugabannin Afirka Ta Kudu, Malaysia Da Colombia Sun Yi Kira Da A Kawo Karshen Laifukan Isra’ila
  • Amurka : Kungiyar DAWN Ta Bukaci ICC Ta Binciki Biden Kan Laifin Hada Kai Da Isra’ila A Laifukan Gaza
  • Nebenzia : Hare-haren Sojojin Isra’ila a Lebanon da Syria na kara dagula lamura a yankin
  • EFCC Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China 16 Da Ake Zargi Da Aikata Zamba Ta Yanar Gizo A Legas