Taron Sin Da Afrika A Alkahira Ya Bayyana Muhimmancin Kyautata Dangantakar Bangarorin Biyu
Published: 28th, February 2025 GMT
Taron lakca karo na 22 na kasar Sin da aka yi jiya Laraba a birnin Alkahiran Masar, ya hada malamai Sinawa da na kasar da jami’ai sama da 200, inda suka tattauna don gane da zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika, wajen daukaka zamanantar da kasashe masu tasowa.
Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika da cibiyar Confucius ta jami’ar Suez Canal ta Masar ne suka karbi bakuncin taron mai taken “Zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika domin jagorantar zamanantar da kasashe masu tasowa.
Tattaunawar ta kuma jaddada batun kara inganta hadin gwiwar Sin da Afrika yayin da ake fama da sauye-sauye a duniya.
Da yake tsokaci, Hassan Rajab, daraktan cibiyar Confucius ta jami’ar Suez Canal, ya nanata raya al’adun bangarori daban daban a matsayi mai muhimmanci ga dangantakar Sin da Afrika, yana mai alakanta ta da shawarar wayewar kan al’ummar duniya da Sin ta gabatar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia
Ya kara da cewa, CMG ta dade tana kasancewa ingantacciyar gada dake inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, kuma ya yi imanin cewa, hadin gwiwarsu a wannan karo zai kara karfafa daddaden dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp