CMG Ya Kaddamar Da Gasar Basirar Mutum-mutumin Inji Ta Duniya
Published: 28th, February 2025 GMT
A ranar 27 ga wata ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kaddamar da gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya a birnin Beijing.
Babban daraktan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, masana’antar mutum-mutumin inji ta zama wata muhimmiyar alama ta auna matsayin wata kasa ta fuskar kimiyya da fasahar kere-kere da kuma masana’antar kere-kere na babban mataki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su iya bin tafarkin zamanantarwa da ya sabawa na yammacin duniya.
A nasa bangare kuwa, daraktan hukumar lura da harkokin waje na kasar Masar Ezzat Saad, cewa ya yi shawarar da Sin ta gabatar ta aiwatar da manufofin zamanantar da duniya, ta samar da karin sassan hadin gwiwarta da kasashen Afirka, tare da yayata kusancin sassan biyu ta fuskar amincewa da juna da hadin gwiwarsu.
Saad ya ce, ta hanyar dandaloli irin na wannan taron, sassan biyu sun samu zarafin karfafa alakar al’adu, da ingiza kafuwar kawance na tsawon lokaci bisa tushen cimma moriyar bai daya da kara fahimtar juna. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp