Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa har yanzu ana iya biyan kudin kujeran aikin Hajji ta hannun hukumar.

 

Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta shafin sada zumunta na hukumar.

 

Ya yi kira ga wadanda har yanzu suke da bukatar zuwa Hajji su tuntubi jami’an hukumar a dukkan kananan hukumomi ashirin da uku na jihar ko su ziyarci hedikwatar hukumar dake kan titin Katsina, a cikin garin Kaduna.

 

Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa mutum dubu uku da dari hudu da sittin (3,460) ne suka biya kudin Hajji ta hannun hukumar.

 

Ya kuma kara da cewa kudin Hajji ya kama naira miliyan takwas da dubu dari hudu da hamsin da bakwai da dari shida da tamanin da biyar, da Kobo hamsin da tara (₦8,457,685.59).

 

Rel/Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Har Hukumar Jihar

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Biya  Sama Da Naira Miliyan 730 Ga Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya

Hukumar fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomin jihar ta fara biyan sama da naira miliyan 733 ga  ma’aikata sama da 280 da suka yi ritaya da kuma ‘yan uwan ​​ma’aikatan da suka rasu.

Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a ofishin fansho da ke Dutse babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa kudaden sun hada da na barin aiki,  da na ma’aikatan da suka mutu.

A cewarsa, ma’aikatan 281 sun hada da na jiha, da kananan hukumomi da na hukumar ilimi, wadanda suka yi ritaya na son rai ko kuma sun kai shekarun ritaya ko kuma wadanda suka mutu suna aiki.

Dakta Bilyaminu Shitu ya ci gaba da bayanin cewa  za a biya ma’aikata 208 da suka yi ritaya daga aiki sama da naira 542, yayin da za a biya sama da Naira miliyan 144 ga ‘yan uwan ​​wadanda suka mutu a bakin aiki su 47.

A cewarsa, rukunin karshe su ne ma’aikata 26 da suka yi ritaya daga aiki kuma suka fara karbar fansho duk wata amma sun mutu kafin su kai wa’adin mafi karancin shekaru biyar bayan sun yi ritaya.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa jihar Jigawa  na daya daga cikin jihohin da ke da kyakkyawan tsarin fensho mafi inganci a kasar nan, duba da yadda ta ke kokarin biyan wadanda suka yi ritaya ba tare da wata matsala ba kuma akan lokaci.

Ya ce wannan gagarumin ci gaba ya nuna irin yadda gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwar ‘yan fanshonta da kuma muhimmancin tabbatar da biyan hakkokin wadanda suka yi wa jihar hidima.

Shugaban ‘yan fanshon ya ce, hukumar ta jajirce wajen tabbatar da biyan kudaden fansho cikin lokaci da inganci kuma tana sa ran za ta ci gaba da yin sabbin abubuwa da nufin inganta jin dadin ‘yan fanshonta.

Biyan kudaden da aka gudanar a hedikwatar hukumar fansho ta jihar Jigawa dake Dutse, wani bangare ne na kokarin karrama kwazon ma’aikatan gwamnati da suka sadaukar da kai wajen yi wa jihar hidima.

Shugaban hukumar ya kuma yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa irin goyon bayan da yake bai wa hukumar.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wadanda aka biya hakkokin nasu, sun nuna jin dadinsu da yadda aka biya su akan lokaci.

Sun yi nuni da cewa, biyansu kudaden  zai ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu da kuma inganta rayuwarsu a lokacin ritaya.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura
  • Helikwaftan farko ƙirar Najeriya zai fara aiki —NASENI
  • Gwamna Sule Ya Hori Masu Ziyarar Ibada Ta Kirista Su Zama Jakadu Na Gari
  • Gwamna Namadi Ya Nada Jami’an Alhazai 27 Tare Da Kara Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajji
  • Gwamnatin Jigawa Ta Biya  Sama Da Naira Miliyan 730 Ga Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajji
  • Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Nemi Hadin Kan Al’ummar Jihar Jigawa
  • Hukumar JSPCACC Ta Kwato Kudaden Gwamnati Sama Da Naira Miliyan 300
  • Majalisar Dokoki Ta Amince Da Kasafin Kudin 2025 Na Kananan Hukumomin Kaduna 23