NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki
Published: 28th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Al’ummar Musulmi na yin azumi ne bisa dalilan addini kamar yadda Allah Ya yi umarni don samun lada.
Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka haɗa da inganta ƙarfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki ba ya bukata.
A taƙaice dai, ba kawai lada mai azumi ke samu ba, har da samun lafiyar jiki da na ƙwaƙwalwarsa.
NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son HaihuwaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan alaƙar da ke tsakanin yin azumi da kuma lafiyar jikin mutum.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: lafiya lafiyar jiki Watan Azumin Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Da Ghana Sun Jaddada Aniyarrsu Wajen Kara Fadada Alakarsu A Dukkanin Bangarori
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun tattauna batutuwa da dama domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka.
An gudanar da ganawar ne a Abuja bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban birnin Ghana.
Wannan dai ya zo ne watanni biyu bayan rantsar da Mahama bayan day a sake komawa kan karagar shugabancin kasar Ghana.
Daga cikin muhimman batutuwa da shugabannin kasashen na Najeriya da Ghana suka yi dubi a kansu, hard a yadda za a kara karfafa alakoki a dukkanin bangaroria tsakanin kasashen biyu.
Baya ga haka kuma sun tabo batun rarrabuwar kawuna da aka samua tsakanin mabobin kungiyar ECOWAS, da kuma matakan day a kamata a dauka domin dinke wannan baraka, da hakan ya hada hard a shiga tattaunawa da kasashen da suka balle suka kafa nasu kawancen, wato Nijar, Burkina Faso da kuma Mali, domin samun fahimtar juna da kuma yin aike tare domin ci gaban yankin da al’ummominsa.