An Fara Tattaunawa Tsakanin Isra’ila Da Hamas Kan Mataki Na Gaba Na Tsagaita Wuta
Published: 28th, February 2025 GMT
Kasar Masar ta ce an fara tattaunawa tsakanin Isra’ila da Hamas kan mataki na gaba na tsagaita wuta a Gaza.
Ma’aikatar yada labaran kasar Masar ta fada a jiya Alhamis cewa, tawagogin Isra’ila, Qatar da Amurka na birnin Alkahira domin tattaunawa mai zurfi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
“Bangarorin da abin ya shafa sun fara tattaunawa mai zurfi don tattaunawa kan matakai na gaba na yarjejeniyar tsagaita wuta, a ci gaba da kokarin tabbatar da aiwatar da fahimtar juna da aka amince da su a baya,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa, masu shiga tsakani suna tattaunawa kan hanyoyin da za a iya “inganta isar da kayayyakin jin kai” zuwa yankin Falasdinu da yaki ya daidaita.
A ranar Alhamis, ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce wata tawaga za ta je Masar domin ganin ko akwai halin tattaunawa kan tsawaita wa’adin zangon farko na tsagaita bude wuta da zai kare nan da kwanaki biyu.
Jami’an gwamnatin sun ce suna neman tsawaita matakin farko, inda Hamas za ta sakin ‘yan Isra’ila guda uku a kowane mako domin musayar Falasdinawa da Isra’ila ke rike da su.
Majalisar ministocin Isra’ila na fuskantar matsin lamba daga jama’a na su tsaya kan tsagaita bude wuta don ‘yantar da sauran fursunonin.
Matakin na farko na tsagaita wutar dai zai kare ne a ranar Asabar.
Kimanin mutane 58 ne Hamas ke tsare da su har yanzu a Gaza, ciki har da 34 da sojojin Isra’ila suka ce sun mutu.
Kungiyar ta Hamas dai ta ce a shirye take ta sako dukkan sauran mutanen da ta ke garkuwa da su gabadaya idan har aka cimma yarjejeniyar a matakin na biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tace Yarjeniya Da Amurka Mai Yuwa Ne Idan Da Gaske Take
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata halarci zaman tattaunawa da kasar Amurka kan shirin kasar na makamashin Nukliya tare da fatan bangaren Amurla ma tana bukatar cimma yarjeniya da ita, matukar Amurka bata kawo wani abu wand aba zai yu Iran ta amince ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin Mosco a lokacinda shi da tokwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov suke amsa tambayoyin yan jarida.
Ministan ya kara da cewa tawagarsa zata je taron birnin Roma tare da fatan tattaunawar zata yi kyau.
Ya kuma kara da cewa takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda Amurka ta dorawa kasar da kuma yin kalamai biyu dangane da tattaunawa da kuma barazana da take wa JMI ba alamu ne na kekyawar niyyar Amurka ba, amma zamu ci gaba da tattaunawar don ganin inda za’a itsaya.
A ranar Asabar 12 ga watan da Afrilun da muke ciki ne aka gudanar da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka zagaye na farko a birnin Mascat na kasar Omman.