Jigawa Ta Kebe Wuraren 57 don Kare Rikicin Manoma da Makiyaya
Published: 28th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga cikin wuraren kiwo guda 400 da ke jihar, ta duba 57 domin dakile rikicin manoma da makiyaya a jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a wajen bude taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen kiwo tare da hadin gwiwa da kwamitin shugaban kasa na aiwatar da gyara harkokin kiwon dabbobi da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar.
Ya ce baya ga samar da tsarin doka na kare wuraren kiwo, manufar za ta kuma tabbatar da amfani da albarkatun kasa mai dorewa a jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa ta kuma dauki ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi 300 na al’umma domin su samar da ayyukan ci gaba ga manoma domin inganta harkar noma a jihar.
“Mun dauki aiki tare da horar da ma’aikatan kula da lafiyar dabbobi 300 na al’umma don gudanar da asibitocin kula da dabbobi ta wayar hannu guda 300 a fadin jihar kuma kawo yanzu ra’ayoyin da aka bayar kan hakan ya gamsar da su.
“Mun kuma yi wa dabbobi sama da dubu 560 allurar rigakafi a karkashin shirinmu na rigakafi na yau da kullun, muna ba su kariya daga cututtuka da kuma inganta sana’arsu.
“Wannan matakin ba wai kawai ya inganta kiwon dabbobi ba, har ma ya kara samar da kudin shiga ga manoman mu ta yadda kiyon dabbobi ya dore,” in ji Gwamnan.
Ya yi nuni da cewa ayyukan da gwamnatin jihar ke yi a fannin kiwo na ci gaba da samun sakamako mai kyau a kudurin kawo sauyi da inganta tasirinsa ga tattalin arzikin jihar.
“Yayin da muke shirin samar da ingantaccen tsari mai inganci na Kiwo ga Jiha, abin farin ciki ne a lura cewa ayyukan da muka yi a fannin kiwo sun ci gaba da samun sakamako mai kyau.
Namadi ya jaddada cewa, “Labarin nasarorin da muka samu wajen kafa ginshikin ci gaba mai dorewa sun hada da karfafa hanyoyin ganowa da wuri, da sassautawa da warware rikicin manoma da makiyaya tare da mai da hankali kan wuraren da ake samun matsala a tarihi,” Namadi ya jaddada.
Malam Umar Namadi ya yi alkawarin dorewar hadin gwiwa tsakanin hukumar manoma da makiyaya ta jihar Jigawa da kwamitin tsaro na masu ruwa da tsaki a bangarori da dama domin wanzar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya domin dorewar samar da ci gaba a fannin kiwo.
KARSHE/USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa manoma da makiyaya
এছাড়াও পড়ুন:
Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu
Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia.
Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa.
Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu.
“Kamar yadda aka bayyana a ranar Laraba 26 ga watan Maris 2025, jimillar kuɗin da aka tattara sun kai Naira miliyan 839. Bisa ga kididdiga da aka yi, kowanne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kai tsaye zai karɓi kimanin Naira miliyan huɗu.
“Ga waɗanda suka rasu, za a ba da kuɗin ga iyayensu ko magadansu, yayin da waɗanda suka tsira za su karɓi nasu da kansu.
“Kayan tallafin da aka riga aka tara, musamman abinci da sauran kayayyakin bukata, tuni an raba su ga waɗanda suka shafi lamarin“, in ji shi.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa akalla mutane 210 ne lamarin ya ritsa da su, inda 100 daga cikinsu suka mutu nan take.
“An tabbatar da cewa mutane 33 daga cikin waɗanda suka rasu magidanta ne, kuma 31 daga cikinsu sun bar ‘yaya. Jimillar matan da suka rasa mazajensu sakamakon lamarin sun kai 42, yayin da yaran da suka zama marayu suka kai 133″, in ji Gwamna Namadi.
A yayin jajantawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamnan ya yi kira ga direbobin manyan motocin dakon mai da sauran masu amfani da tituna su kasance masu taka tsantsan domin gujewa sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.
“Iftila’in da ya afku a Majia ya koyar da mu darussa masu yawa, wanda muke fatan jama’a da masu ruwa da tsaki, musamman ma waɗanda ke harkar sufuri, za su dauki darasi“. Inji shi.
Gwamnan ya kuma shawarci waɗanda suka karɓi tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, musamman wajen kafa sana’o’i.
Usman Muhammad Zaria