Sako daga Alawiyya Jilani Jihar Kano:
Ina gaishe da Mummy da Abba, da kannena Zuhra, Sajida, Alhaji, da dukkanin kawayena na islamiyya dana boko wadanda muka kammala dukka, ina gaida Khadija (Sweet Bala), ina gaishe da Siyama Abdul, ina gaishe da Aunty Hajara da sauran ‘yan’uwa da fatan sakon ya iso gare ku kuma da fatan kun yi juma’a lafiya.
Sako daga Balaraba Ibrahim Jihar Kaduna:
Assalam.. Dan Allah a gaishe mun da Sisi ‘yar fucika uwar tsokana, da Hajiya Hazira, da Aunty Amina mai sakwara, ina gaishe da baby nice, da Binta kwaram da sauran wadanda ban gaisar ba wanda suka sanni.
Sako daga Yusuf Uba Muhammad Jihar Kano:
Haj. Rabi’at dan Allah a mikan sakon gaisuwata zuwa ga Baffa Salisu da abokaina kamar su; Zayyanu, Hassan, Fatuhu, Mansur, Aliyu dan ball, su Idris, Shafi’u dake garin Katsina, Alkhairin Allah ya kai masa, sannan ina gaishe da budurwata Maryam Baby, Allah ya sa ta yi juma’a lafiya.
Sako daga Bilyaminu Ahmad Jihar Kaduna:
Sakona zuwa ga dukkanin al’ummar musulmi ne na fadin duniya, ina gaishe da kowa kuma ina yi mana addu’ar fara azumi lafiya mu gama lafiya dan isar Annabi da alkur’ani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajji
Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025.
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi a Otal din Grand Central.
Alhaji Danbappa ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar kudaden maniyyata har zuwa ranar daya ga watan Ramadan.
Ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yau 25 ga watan Fabrairun 2025, hukumar ta bada sama da naira biliyan 22 ga hukumar alhazai ta kasa a madadin Alhazan jihar Kano.
Bugu da kari, babban daraktan ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa gaugawar daukar mataki na magance bukatun hukumar a duk lokacin da ake bukata.
A nasa jawabin shugaban hukumar gudanarwar Alhaji Yusif Lawan ya bukaci ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu.
Abdullahi Jalaluddeen