Gwamnatin Kano Ta Shirya Taron Bita Don Jami’an Watsa Labarai
Published: 28th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai.
Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani.
Da yake bayyana bude taron, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada kudirin gwamnati na ganin sun kware a fannin sadarwa.
Ya jaddada mahimmancin kayan aikin zamani,tare da haɗin gwiwar kafofin watsa labarun, da sadarwa ta hanyar bayanai don tabbatar da ingantaccen kuma da yada bayanai akan lokaci.
Ya kuma bayyana muhimmiyar rawar da Jami’an Watsa Labarai ke takawa wajen tsara fahimtar jama’a, tabbatar da gaskiya, da kuma kiyaye amanar jama’a.
Kwamishinan ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da bayar da tallafin da bayar da horon, inda ya bayyana cewa gwamnati ta bada fifiko wajen bunkasa dan adam a matsayin ginshikin gudanar da shugabanci na gari.
Babban sakataren ma’aikatar, Adamu Bala Muhammad, ya ja hankalin mahalarta taron da su kara yawan wannan dama da kuma amfani da ilimin da suka samu wajen inganta sadarwa da bayar da hidima ga gwamnati.
Shugaban Hukumar NIPR na Jihar Kano, Aliyu Yusuf, ya yabawa gwamnatin jihar bisa daukar nauyin gudanar da taron bitar tare da amincewa da yin rajistar duk jami’an yada labarai na NIPR.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, taron ya kunshi kwararrun masu gudanarwa daga hukumar NIPR, wadanda za su karfafa wa mahalarta taron su kara kaimi da dabarun gudanar da ayyukansu.
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yada Labarai
এছাড়াও পড়ুন:
APC Ta Gaza Gudanar Da Taron NEC Cikin Shekaru Biyu – PDP Ta Zarge Su
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp