HausaTv:
2025-02-28@16:38:50 GMT

Shugaban kasar Guinea-Bissau a ya yi wata ganawa da shugaban kasar Rasha

Published: 28th, February 2025 GMT

Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo sun tattauna a fadar Kremlin, yayin da ‘yan adawar Guinea-Bissau suka sha alwashin gurgunta kasar gabanin zabe.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, sun yi shawarwari a fadar Kremlin, a wani sabon salo na yunkurin da Moscow ke yi na kulla huldar tattalin arziki da tsaro da kasashen yammacin da tsakiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya habarta cewa, hamshakin attajirin nan na Rasha Oleg Deripaska ya halarci tattaunawar da shugabannin biyu suka yi.

Kafofin yada labarai sun ambato wani minista a Guinea-Bissau, ya ce, Kamfanin aluminium na Rasha Rusal yana sha’awar gina layin dogo da tashar jiragen ruwa a kasar, da kuma binciken ma’adanai na bauxite.”

A wani labarin kuma, ‘yan adawa a kasar Guinea-Bissau sun lashi takobin kawo cikas ga harkokin rayuwa a kasar dake yammacin Afirka a yau Alhamis, sakamakon takaddamar da ta kunno kai dangane da wa’adin mulkin shugaba Umaro Sissoco Embalo na shekaru biyar zai kare.

Shugabannin ‘yan adawa sun ce a cewar Reuters, wa’adin Embalo zai kare ranar Alhamis, yayin da kotun kolin shari’a a Guinea-Bissau ta yanke hukuncin cewa wa’adin ta ya kare a ranar 4 ga Satumba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Shugaban kasar

এছাড়াও পড়ুন:

Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman

Wata Babbar Kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ake tuhuma da almundahana.

A ranar Alhamis, Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin sakin Farfesa Usman daga gidan gyaran hali na Kuje bayan an cika sharuɗan belinsa.

Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki

Hukumar EFCC ce, ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗaɗe.

Ana zargin ya amince wajen sayen motoci a kan Naira miliyan 49.2 maimakon Naira miliyan 30 da aka ware a matsayinsa na shugaban NHIS a 2016.

EFCC, ta kuma ce Farfesa Usman ya bai wa wani kamfani mai suna Lubekh Nigeria Limited kwangilar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta Naira miliyan 17.5 ta hannun ɗan uwansa, Khalifa Hassan Yusuf.

Duk da haka, Farfesa Yusuf ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Sin Ya Gana Da Sakataren Majalisar Tsaron Rasha
  • Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara
  • Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano
  • Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman
  • Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza
  • Sheikh Na’im Kasim Ya Gana Da Ministan Harkokin wajen Kasar Iran Da Shugaban Majalisar Dokoki
  • Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje
  • Shugaban Iran ya sha alwashin inganta hadin gwiwa da Rasha
  • Shugaban Zimbabwe Ya Kaddamar Da Yankin Masana’antu Da Sin Ta Zuba Jari