Pezeshkian: Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Kara Karfafa Alakokinsu
Published: 28th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce inganta hadin kai da alaka tsakanin kasashen musulmi da suka hada da Iran da Malaysia na daga cikin abubuwan da ake bukata a halin da ake ciki a duniya.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da ministan harkokin wajen Malaysia Dato’ Seri Utama Haji Mohamad Bin Haji Hasan a birnin Tehran a wata ziyara da ya kai kasar Iran.
Ya ce a halin yanzu gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana aiwatar da abin da take yin a laifuka da wuce gona da iri a yankin saboda kan musuylmi ba hade yake ba.
Ya kara da cewa samar da hadin kai tsakanin jami’ai da ‘yan siyasar kasashen musulmi zai taka muhimmiyar rawa wajen kawar da bambance-bambance, rashin fahimta da talauci a cikin kasashen musulmi.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take domin kara fadada hanyoyin sadarwa da kasashen musulmi ciki har da Malaysia a dukkan fannoni in ji shugaban na Iran.
A ci gaba da jawabin nasa, Pezeshkian ya yi nuni da cewa, an gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa na kasashen Iran da Malaysia karo na 8 a birnin Tehran a safiyar Laraba bayan shafe shekaru 17 ana yin irin wannan taro.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Malaysia ya ce alakar da ke tsakanin Tehran da Kuala Lumpur ta ginu ne bisa fahimta da ‘yan uwantaka.
Ya bayyana aniyar Malaysia na bunkasa alaka da Iran da kuma amfana da karfin Jamhuriyar Musulunci ta fuskar kimiyya, fasaha, ilimi, kayan abinci da noma.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Diblomasiyyar Kasashen Rasha Da Amurka Zasu Sake Haduwa A Birnin Istambul A Gobe
Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu.
Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko. Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau.
A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana ruwa guda a ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da Mosco.
A ranar 18 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne a karon farko tun bayan fara yakin Ukraine jami’an diblomasiyyar kasashen biyu suka hadu a birnin Riyad na kasar Saudiya.