Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Nemi Goyon Bayan Sarkin Zazzau Don Nasarar Aikin Hajjin Bana
Published: 28th, February 2025 GMT
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta yaba da gudunmuwar da Gwamnatin Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ke badawa wajen samun nasarorin da aka samu kwanan nan.
An bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar girmamawa da Shugaban Hukumar Jindadi Alhazai na Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar ya jagoranta tare da tawagar Kwamitin Musamman na Hajji da shugabannin ga Sarkin Zazzau, Malam Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya.
Babban burin ziyarar shi ne neman ci gaba da samun goyon baya da addu’o’in Sarkin don samun nasarar ayyukan Hajji na shekarar 2025.
Malam Salihu ya nuna godiya sosai ga gudunmuwar da Sarkin ya ba da a baya kan shirye-shiryen Hajji, tare da jaddada muhimmancin cigaba da wannan hadin kai.
Ya ce, “Goyon bayan Gwamnatin Jihar Kaduna ga jin dadin alhazanmu abin alfahari ne. Tallafi daga dukkan fannoni, ciki har da na kudi ya taimaka mana sosai wajen cimma nasarorinmu. Wannan irin goyon bayan ya bambanta Hukumar ta Kaduna da takwarorinta.”
Malam Salihu ya kara da cewa hukumar ta riga ta yi rijistar alhazai 3,480 don lokacin Hajji mai zuwa kuma ta kaddamar da shirin wayar da kan alhazai.
Wannan shirin yana da nufin ilmantar da alhazai game da yadda ake gudanar da ibadar Hajji, dokoki, da koyarwar addinin Musulunci.
A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya yabawa Kwamitin Musamman na Hajji kan gyare-gyaren da suka kawo a hukumar.
Ya jaddada cewa wadannan gyare-gyaren suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa alhazan sun amfana da kudaden da suka kashe wajen tafiya Saudiyya.
Sarkin ya yi kira da a ilmantar da alhazai kan haramcin daukar kaya haram zuwa Kasar Saudiyya don kauce wa samun matsala da hukumomin Saudiyya.
Ya kuma roki Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Saudiyya da su ci gaba da yin aiki tare da Hukumar Hajji ta Kasa domin tabbatar da cewa alhazan Najeriya sun samu kima da mutunci a tsawon zamansu.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Nemi Goyon Bayan Sarkin Nasarar
এছাড়াও পড়ুন:
Helikwaftan farko ƙirar Najeriya zai fara aiki —NASENI
Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa.
Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka.
Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba.
Manajan Ayyuka a Cibiyar Binciken Kera Jirage na NASENI da ke Kaduna, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa Ya ci gaba da cewa, “yanzu mun kai matakin ƙarshe kuma nan gaba kaɗan za mu yi gwajin tashin helikwaftan farko ƙirar Najeriya.”
Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansaYa ƙara da cewa suna ƙera jiragen ne ta hanyar inganta ayyuakansu daga abin da aka saba.
Ya ce, “yanzu muna aikin ƙera jirage marasa matuƙa da helikwafta ’yar Najeriya da sauransu.
“Wasu daga kayayyakin da muke amfani da su an ƙera su ne a ƙasashen da suka ci gaba.
“Ta hanyar aikin injiniya da ƙwarewar kimiyya muka hada waɗanna kayayyaki da na’urori,” in ji shi.