An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya
Published: 28th, February 2025 GMT
Hukumomi a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin yau Juma’a.
Hakan na nuni da cewa azumin bana zai fara a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025.
Shafin Haramain Sharifain ne, ya tabbatar da wannan sanarwa, yayin da aka ga jinjirin watan a wurare daban-daban na ƙasar.
Wannan na nufin cewa Musulmai a Saudiyya za su fara azumi a ranar Asabar.
Hakazalika, ƙasashen Qatar da Oman sun sanar da cewa za su fara azumin Ramadan a wannan ranar Asabar.
A yayin da ake shirin shiga wannan wata mai alfarma, an yi kira ga Musulmai da su yi amfani da lokacin azumi wajen ƙara yawan ibada, yin kyawawan ayyuka, da taimaka wa marasa galihu, duba da yanayin tattalin arziƙin duniya.
Ana sa ran cewa, Saudiyya da wasu ƙasashe, za a fara azumin Ramadan a sassa daban-daban na duniya a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jinjirin Wata Ramadan Saudiyya ranar Asabar
এছাড়াও পড়ুন:
An ga watan Sallah a Saudiyya
An ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya.
Shafin Haramain na mahukuntan da ke kula da Masallatan Harami na Makkah da Madinah ne ya tabbatar da hakan