Shugaban Sin Ya Gana Da Sakataren Majalisar Tsaron Rasha
Published: 28th, February 2025 GMT
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Sergei Shoigu, sakataren majalisar tsaro ta kasar Rasha, a nan birnin Beijing.
Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce, Sin da Rasha sun kasance masu tuntubar juna a dukkan matakai, da aiwatar da matsayar da suka cimma da shugaba Putin da hadin gwiwa mai muhimmanci da moriyar juna tare da zurfafa hadin gwiwarsu a kai a kai, domin taimakawa muradunsu na bai daya na samun ci gaba da farfado da kasashen biyu.
A nasa bangare, Sergei Shoigu ya ce, Sin da Rasha sun kai wani matsayi da ba a taba gani ba, kuma ba su yi hakan don muzgunawa wata kasa ba. Ya ce, haduwar Sin da Rasha ta taka muhimmiyar rawa a duniya, kuma ta nuna misalin dangantaka tsakanin manyan kasashe. Ya ce, Sin da Rasha za su ci gaba da kasancewa masu aminci da juna da tattaunawa bisa daidaito, kuma muhimmin hadin gwiwar dake tsakaninsu, ya dace da muradunsu na bai daya. Bugu da kari, ya ce, Rasha za ta aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen 2 suka cimma tare da karfafa dangantakarta da Sin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Sin da Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa
Shugabannin Jam’iyyar APC, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, da sauran manyan jagorori, sun gana a daren Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
An gudanar da taron ne domin shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a yi a yau a hedikwatar APC.
Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin AkpabioWannan shi ne taron farko da za a yi taron tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
A bara, an tsara shirya waɗannan taruka ne a watan Satumba, amma aka ɗage su ba tare da saka sabuwar rana ba.
A baya-bayan nan, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya soki shugabannin jam’iyyar da rashin shirya taruka, inda ya ce APC ta fara rabuwa da aƙidun da aka gina ta a kai.
An fara taron ne da misalin ƙarfe 7:30 na dare, bayan isowar Shugaba Tinubu.
Batutuwan da aka tattauna sun haɗa da shirin gudanar da babban taron jam’iyyar, matsalolin shari’a da ke shafar jam’iyyar, cibiyar nazari da tsara manufofin APC da sauransu.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Sauran sun haɗa da wasu gwamnoni kamar Hope Uzodinma (Imo), Babajide Sanwo-Olu (Legas), Dapo Abiodun (Ogun), da Babagana Umar Zulum (Borno).
Haka kuma, mambobin kwamitin jam’iyyar da tsohon shugaban APC na ƙasa, Cif Bisi Akande, sun halarci taron.