An ga watan Ramadan a Najeriya — Sarkin Musulmi
Published: 28th, February 2025 GMT
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Juma’a, wanda hakan ke nufin ranar Asabar, 1 ga watan Maris, ita ce daya ga watan Ramadan 1446 Hijira a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmi, ya karanta a fadarsa, ya bayyana cewa an samu sahihan bayanai daga kwamitocin ganin wata da shugabannin addinin Musulunci a sassa daban-daban na kasar nan.
a dalilin haka, ya ayyana fara azumin watan Ramadan daga safiyar Asabar.
Haka nan, hukumomin Saudiyya ma sun tabbatar da ganin watan, inda suka ayyana Asabar a matsayin daya ga watan Ramadan a kasar.
Kira Ga Musulmi
Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi riko da ibada, addu’a da taimakon marasa galihu a wannan wata mai alfarma.
“Yana da matukar muhimmanci a cikin wannan wata mu kasance masu sadaukarwa, taimakon mabukata da kuma yawaita addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban kasa,” in ji shi.
Ya kuma bukaci masu hali da su tallafa wa talakawa da gajiyayyu, musamman da abinci da sauran kayayyakin bukatu domin saukaka musu azumi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ga watan Ramadan Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Hamayyar Siyasar A Kasar Turkiya Suna Ci Gaba Da Yin Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
A jiya Asabar dubun dubatar ‘yan hamayyar siyasa su ka yi gangami a birnin Stanbul bayan da jam’iyyar “National Party” ta gayyace su, domin ci gaba da yin tir da kamun da aka yi wa Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin na Stanbul.
Shugagan jam’iyyar “Turkish National Party’ ta adawa, Uzgur Ozil ya bayyana cewa adadin wadanda su ka halarci gangamin sun kai miliyan 2.2.
Daga cikin mahalarta gangamin da akwai mata da mahaifan Akram Ima wadanda su ka rika bayar da taken cewa za a ci gaba da yin gwgawarmaya ako’ina.”
Tun da asubahin jiya Asabar ne dai mutane su ka fara yin tururuwa a cikin birnin na birnin Sitanbul suna dauke da tutocin turkiya da kuma hotunan Mustafa Kamal Ataturk wanda ya kafa jamhuriyar Turkiya.
Tun bayan da aka kama Imam Uglu a ranar 19 ga watan Maris ne dai kasar ta Turkiya ta fada cikin dambaruwar siyasar wacce an dade ba a ga irinta ba.
Shugaban jam’iyyar hamayyar ya fadawa jaridar “ Lo Monde” ta Faransa cewa a kowace Asabar za su zabi garin da za su gudanar da Zanga-zanga,sannan kuma da kowane marecen Laraba a cikin birnin Sitanbul.