Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Nabamamu a Zamfara
Published: 28th, February 2025 GMT
Dakarun Sojin ‘Operation FANSAN YANMA’, sun kama Ƙasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu, wanda ya addabi al’ummar Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara.
Dakarun sun kai farmaki Hegin Mahe, Ruwan Bore, garin Mada, a Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan KanoBayan musayar wuta, sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga, yayin da Nabamamu ya tsere zuwa cikin wani gida, amma daga ƙarshe dakarun suka cafke shi.
Bayan kama shi, ɗaya daga cikin yaransa, Bakin Malam, ya jagoranci kai harin ramuwar gayya wasu ƙauyuka, wanda ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa.
Sai dai dakarun sun mayar da martani, inda suka fatattaki ’yan bindigar, tare da ƙara jibge sojoji don tabbatar da tsaro a yankin.
Nabamamu, ya kasance almajiri ne, daga baya ya zama hatsabibin ɗan bindiga wanda ya yi sanadin ajalin mutane masu yawan gaske.
Ya jagoranci sama da mayaƙa 100, inda yake karɓar haraji daga hannun mazauna wasu ƙauyuka, kuma yana da alaƙa da masu yi wa wasu mahara safarar makamai a yankin.
Kama shi na iya rage ƙarfin ’yan bindiga a Zamfara, yayin da sojoji ke ƙara ƙaimi domin kawar da barazanar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Artabu dakaru Ɗan Bindiga musayar wuta Zamfara yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Gobe take Sallah a Nijeriya
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.
Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi.
Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.