MDD Ta Bayyana Cewa Yara Fiye Da 100,000 Ne Suka Ka Yi Rijistan Fara Karatu A Makarantun Gaza Na Sabuwar Shekarar Karatu
Published: 28th, February 2025 GMT
Kakakin Majalisar dinkin MDD Stephane Dujarric ya bada sanarwan cewa yana makaranta a Gaza fiye da 100,000 suka fara karatu a makarantu a yankin a ranar 23 ga watan Fabrayrun da muke ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’in MDD yana fadar haka a jiya Alhamis kwanaki huda da fara karatu a yankin na Gaza, bayan tsekon da aka samu saboda yakin da HKI ta dorawa kasar na tsawon shekara guda da watanni.
Dujarric ya bayyana cewa a halin yanzu makarantu 165 suka bude kofofin su ga yan makaranta a gaza, kuma ga mafi yawansu wannan shi ne karo na farko da suka shiga aji a cikin watanni 16 da suka gabata.
Jami’an gwamnati a Gaza sun bayyana cewa HKI ta rausa kashi 85% na makarantun Gaza a cikin yakin da ta dorawa yankin daga cikin watan Octoban shekara ta 2023.
Labarin ya kara da cewa akalla daliban makaran 12,800 da malaman makaranta da ma’aikatan makarantu 800 suka rasa rayukansu a yankin na shekara guda da watanni. Sannan HKI ta rusa cibiyoyin karatu akalla 1,166 a wannan yakin. Banda haka yakin ya jawo asarar dalar Amurla billiyon $2 wa bangaren ilmintarwa a Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jakadan Sin A Amurka: Beijing Na Adawa Da Duk Wani Nau’in Karin Haraji Ko Yakin Ciniki
Ya kuma ce, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na yakin karin haraji ko yakin kasuwanci. Kuma wannan ba wai don kare muradu da martabar kasar Sin ba ce kawai, har ma da kare tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci.
A cewarsa, “Idan har wata kasa ta dage kan kakaba mana yakin haraji ko kuma yakin kasuwanci, to tabbas za mu yi gaba-da-gaba da ita ba tare da tsoro ba, kuma tabbas za mu dauki kwararan matakan mayar da martani.”(Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp