Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano
Published: 28th, February 2025 GMT
Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki.
Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin.
An ga watan Ramadan a Najeriya An ga jinjirin watan Ramadan a SaudiyyaAn gano cewar an tura kuɗin filin Naira miliyan 100 a asusun banki na shugaban.
Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kama Mohammed.
Ya tabbatar da cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, a asusunsa.
Sai dai hukumar ta ce ta karɓo kuɗaɗen haba ɗaya.
A cewar hukumar Mohammed, yana bayar da haɗin kai wajen binciken, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin bankaɗo cikakkun bayanai game da badaƙalar.
Hukumar ta jaddada ƙudirinta na yaƙi da cin hanci da tabbatar da gaskiya a tafiyar da shugabanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Badaƙalar Fili Ciyaman Ƙaramar Hukuma Ƙaramar Hukumar Ƙiru rashawa
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi
Dubban jama’a ne suka hallara domin ɗaurin auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar.
Cikin baƙi akwai Shugaban Kamfanin rukuin Media trust Malam Kabiru Yusuf da sauran manyan baƙi suka hallara a birnin domin ɗaurin auren da kuma naɗin sarautar “Makama Babba I da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar.
Masu garkuwa za su mutu ta hanyar rataya a Edo – Okepebolo An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a NejaAlhaji Bala Ahmad babban limamin Bauchi ne ya jagoranci ɗaurin auren, wanda Shettima ya kasance a matsayin waliyyin ɗiyar tsohon gwamnan yayin da Yusuf Yakubu Wanka, Chigarin Bauchi, ya kasance waliyyin angon, Sadiƙ Mohammed Wanka a wajen ɗaurin auren.
Bayan ɗaurin auren, Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu ya naɗa wa tsohon gwamnan rawani a matsayin Makama Babba na farko, sannan ya sa baƙar Alkyabba.
Tun da farko mataimakin shugaban ƙasar, wanda ya sauka a filin jirgin sama na Sa Abubakar Tafawa Balewa ya samu tarba daga gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed da gwamnan Jihar Gombe Mohammed Inuwa Yahaya.
Haka kuma, taron ya samu halartar wasu manyan baƙi da dama, ciki har da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmadu Mu’azu, mataimakin gwamnan Yobe, Shugaban Kamfanin Media Trust Malam Kabiru Yusuf da sarakunan gargajiya da jama’a daga kowane fanni.
Fadar Sarkin dai ta cika maƙil a yayin da sauran manyan baƙi daga sassa daban daban su ma suka halarci bikin, inda aka ɗaura auren Sadiƙ Mohammed Wanka, da Khadijatu Mohammed Abdullahi Abubakar akan sadakin Naira 300,000.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana godiyarsa ga Shettima, Pate, Tuggar da Gwamnan Jihar Gombe da sauran manyan baƙi bisa halartar ɗaurin auren da kuma bikin naɗin sarautar tsohon Gwamna a matsayin Makama Babba na Bauchi na farko.
Ya kuma taya tsohon Gwamnan murna kan abin da ya bayyana a matsayin mafi kyawu kuma wanda ya cancanta saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar.