Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%.

Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo babban yankin kasar a bara ya kai miliyan 131.

9, wanda ya karu da kaso 60.8%, kuma daga cikinsu miliyan 26.94 ’yan kasashen waje ne, sauran kuma sun fito daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan, kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe ya kai dala biliyan 94.2, wanda ya karu da kaso 77.8%. Ban da haka, yawan mazauna babban yankin kasar Sin da suka fita daga kasar ya kai miliyan 145.89, kuma daga cikinsu miliyan 97.12 sun je yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan. (Lubabatu Lei)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

A Cikin Mako Daya An Yi Asarar Naira Biliyan 365 A Kasuwar Sayar Da Hannun Jari

A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43.

Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda  60,782 da masu zuba hannun suka yi.

Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818  sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222.

Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune,  kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da Bankin Jaiz Plc, sun sayar da shiyar da ta kai ta Naira biliyan 1.621, tare da karin Naira biliyan 3.244 da kuma wata  hada-hadar Naira biliyan 1,528.

Hakan ya nuna cewa, an samu karin da ya kai na kaso 49.42 da kuma karin wani kaso 5.11 wanda ya nuna irin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta baki daya a kasuwar a cikin makon.

Kazalika, kamfanin sarrafa abincin dabbobi na Livestock Feeds Plc, ya samu karin farashin shiya mai yawa, inda ya samu kaso 22.16 sai kuma kamfanin Caverton Offshore Support Grp da ya samu farashin shiyar da ta kai karin kaso 15.38.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • A Yau Litinin Ce Aka Gudanar Da Sallar Edi Da Bukukuwan Sallah A Nan Iran Da Wasu Kasashen Musulmi
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Kasashen Yamma Sune Yan Ta’adda Na Gasliya A Yankin
  • Iran: Amurka ta hada kai da Isra’ila wajen kawo cikas ga harkar tsaro a gabas ta tsakiya
  • Gwarzon gasar Alƙur’ani ya Kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina
  • Kamfanonin Kasashen Waje Na Da Imani Kan Ingancin Kasuwar Kasar Sin 
  • Adadin mamata a girgizar kasar Myanmar ya ka 1,644
  • Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu
  • Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
  • A Cikin Mako Daya An Yi Asarar Naira Biliyan 365 A Kasuwar Sayar Da Hannun Jari
  • Najeriya Da Ghana Sun Jaddada Aniyarrsu  Wajen Kara Fadada Alakarsu A Dukkanin Bangarori