Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗi na N54.99trn
Published: 1st, March 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da ya kai Naira tiriliyan 54.99.
A ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025, Majalisar Dokoki ta amince da kasafin bayan tattaunawa da nazari a kansa.
Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aikiA baya dai, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin da ya kai Naira tiriliyan 49.
Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin a ranar Juma’a, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Kasafin kuɗin na 2025 ya ninka wanda aka yi a bara, wanda ya tsaya a Naira tiriliyan 27.5, da ƙarin kashi 99.96 cikin 100.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya ta sanar da hango watan Shawwal, ranar lahadi ce Sallah a kasar
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana.
Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata.
Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.