Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya
Published: 1st, March 2025 GMT
Saɓanin shekarun baya, azumin watan Ramadan na bana ya zo a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa farashin kayan abinci na sauka a sassan Najeriya.
Kayayyakin masarufi irinsu shinkafa da wake da fulawa na daga cikin waɗanda aka fi sarrafawa a watan na Ramadan, kuma su ne masu gwaggwaɓan kaso a faɗuwar farashin.
Farashin kayan masarufi na sauka a wannan karo ne baya kimanin shekara biyu a jere suna tashi a ƙasar.
Haka kuma, ana iya cewa ’yan Najeriya sun saba ganin tashin farashin kaya, musamman na abinci, a gabnin watan Ramadan.
Duk da mutane suna nuna jin daɗinsu da saukar farashin a wannan karon, amma wasu na cewa hakan bai kawo sauƙi ga talaka ba, a wannan lokaci da aka ɗauki haramar ibadar azumi, saboda rashin kuɗi a hannun jama’a.
An ga watan Ramadan a Najeriya An kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a KanoWata matar aure da Aminiya ta zanta da ita ta ce, duk saukar da farashin abinci ke yi, amma ta hatsi ake yi ba ta kayan marmari ba
Ƙarancin masu sayayyaA zagayen da Aminiya ta gudanar a Kasuwar Rimi da ke Kano, ta lura da ƙarancin masu zuwa cefanen azumi a satin jajiberan Ramadan, saɓanin lokutan baya.
Bisa al’ada dai, mata kan yi cefanen kayan abinci na musamman da ake amfani da su a watan azumi, a wasu lokutan ma, har da sabbin mazuban abin ci da sha ga mai gida.
Jiya ta fi yauFatima Muhammad Nasir matar aure ce mai ’ya’ya biyu a Kano, ta kuma bayyana wa Aminiya cewa a kowacce shekara idan ta zo gara bara da bana ake a kan farashin kayan abinci a Najeriya.
“A bangarena kayan abincin da suka fi muhimmanci a watan azumi su ne dankali, mai, fulawa, doya, kayan shayi, da aya, zoɓo, wake, gyadar kunu, da sauransu.
Yanzu ta hatsi ake…“A shekarun baya ina da ƙarfin sayen su nama, kaji, kifi, da doya, da ƙwai amma a bana sai wane da wane.
“Yanzu ta hatsi ake yi ba waɗannan ba. Na baki misali shekaru biyu baya kajin da mai gidan ke saya a kan N7,000 – N11,000 a bana N25,000 zuwa N30,000 ne.
“Gyaɗar kunu a kan N5,000 muka saya kwano ɗaya, aya N1,300, Zoɓo kuma N1,000. Rabin buhun dankali shekaru biyu baya akan N10,000 ne, amma yanzu akan N30,000 ake sayar da shi.”
Ita ma Asma’u Muhammad cewa ta yi tsadar kayan abinci a bana ba kaɗan ba ne idan aka kwatanta da azumin bara.
“Akwai abubuwan da sayen su sai ka ci ka tada kai a yanzu saɓanin baya.
A da, masu girke-girke a soshiyal midiya na yin girkin da muke kallo mu kwaikwaya mu yi a namu gidan, amma yanzu ba komai ne zai yi wu ba.
ƘalubaleWata matsala da a azumin bara aka dinga kuka da ita ce ta tsadar ƙanƙara ba da ma ƙarancinta, inda aka dinga sayen manya a kan N500 zuwa sama, ƙanana kuma N300.
Asma’u ta ce babbar matsalar da ke kawo hakan ba ta wuce matsalar rashin wutar lantarki da ta ƙi ci taƙi cinyewa ba, amma a bana tana fatan za a samu sauyi.
“Ƙalubalen da muka fuskanta a bara shi ne tsadar ƙanƙara da rashin wuta. Mutane sun sha wahala saboda an yi rana sosai kuma sanyin da za ka sha an tsuga masa kuɗi. Amma ina fata a bana haka ba za ta faru ba.”
Ita ma Fatima ta bayyana rashin wutar a matsayin babban ƙalubale, musamman a lokutan buɗa baki da sahur.
“Haka muka dinga sahur da buɗa baki a duhu a bara, saboda rashin wuta. Allah Ya sa a bana ba haka za a yi ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: masarufi Ramadan kayan abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Labarin Bukar, Malamin Da Ya Shafe Watanni 20 Ba Tare Da Albashi Ba A Borno
Sai dai Bukar ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa ya sanar da shugabansa kuma ya bi duk matakan da suka dace, amma har yanzu ba a bi masa haƙƙinsa ba. Ya ce sau da dama an buƙaci ya kawo bayanan asusun ajiyarsa na banki don duba matsalarsa, amma babu wani canji. Duk da cewa shugaban makarantar ya wanke shi daga zargin guduwa daga aiki, har yanzu ba a mayar masa da albashinsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp