Aminiya:
2025-03-01@11:27:45 GMT

Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250

Published: 1st, March 2025 GMT

Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara.

Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya.

Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn

Yayin bikin rabon dabinon, Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Admawy, ya gode wa Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa ƙoƙarinsu na ci gaba da tallafa wa al’ummar Musulmi a faɗin duniya.

Ya jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da taimaka wa Musulmai, musamman a lokacin watan Ramadan.

A bana, Saudiyya ta ware tan 50 na dabino don raba wa a Kano da wasu jihohin Arewa, baya ga tan 60 da aka riga aka aike Abuja a makon da ya gabata.

Ana ci gaba da shirin rabawa don tabbatar da cewa dukkanin kayan sun isa hannun buƙata.

Jakadan Saudiyya, ya kuma bayyana cewa shirin buɗa baki na ƙasar zai fara aiki ne a Abuja a ranar 3 ga watan Ramadan, inda za a raba wa Musulmai masu azumi abinci kyauta.

Ya kuma yi bayani kan irin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarkin ke yi a duniya, inda ya ce tuni cibiyar ta kammala sama da ayyuka 2,500 da darajarsu ta haura dala biliyan bakwai, waɗanda suka amfanar da ƙasashe 91.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Farouk, ya wakilta, ya nuna godiyarsa ga wannan kyauta.

Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta tabbatar da cewa an raba dabinon ga waɗanda suka dace su amfana.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa kyauta Ramadan Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano

Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki.

Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin.

An ga watan Ramadan a Najeriya An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya 

An gano cewar an tura kuɗin filin Naira miliyan 100 a asusun banki na shugaban.

Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kama Mohammed.

Ya tabbatar da cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, a asusunsa.

Sai dai hukumar ta ce ta karɓo kuɗaɗen haba ɗaya.

A cewar hukumar Mohammed, yana bayar da haɗin kai wajen binciken, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin bankaɗo cikakkun bayanai game da badaƙalar.

Hukumar ta jaddada ƙudirinta na yaƙi da cin hanci da tabbatar da gaskiya a tafiyar da shugabanci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Noman Dabino: Jigawa Ta Yi Hadaka Da Saudiyya
  • Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano
  • An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya 
  • Kwara ta Raba Littafai Fiye da Dubu 74 Kyauta Ga Dalibai
  • LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya
  • Gidauniyar Sarki Salman Ta Rab Tallafin Abinci Ga Mutane 2,450 A Kebbi
  • Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano
  • Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙa kayan makaranta a Kano
  • Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino