HausaTv:
2025-03-01@11:32:48 GMT

An Yi Jana’izar Shahidan Hizbullah Fiye Da 100 A Kudancin Lebanon

Published: 1st, March 2025 GMT

A jiya Juma’a ne dai aka yi jana’izar shahidan Hizbullah 130 a garuruwan Aytas-sha’ab da Aytarun da suke da kudancin Lebanon.

Tashar talabijin din al-manar ta watsa taron jana’izar shahidai 95 da su ka yi shahada watanni uku da su ka gabata a yayin yaki da HKI.

A garin Aytrun da shi ma yake a kudancin Lebanon an yi jana’izar shahidai 35.

Dukkkanin jana’izar biyu ta sami halartar dububan mutane daga cikin garuruwan da kuma wajensu.

 A gefe daya, a daidai lokacin da ake gudanar da jana’izar mutanen a garin Aytatun, sojojin HKI sun kai hari a gefen garin, sai dai babu rahoto akan shahada ko jikkatar mutane.

Dan majalisa mai wakilntar Hizbullah a majalisar dokoki Hassan Fadlallah wanda kuma shi ne shugaban bangaren masu goyon bayan gwgawarmaya a majalisar, ya gabatar da jawabi a wurin jana’izar, inda ya bayyana cewa; Shahidan sun kwanta dama ne a fagen dagar kare daukakar al’ummar Lebanon.

A garin Aytas-sha’ab,  an yi taho mu gama mai tsanani a tsakanin dakarun Hizbullah da sojojin mamayar HKI a lokacin yakin 2006, kuma a wannan yakin ma abinda ya faru kenan,’kamar yadda Fadlallah ya bayyana.

Dan majalisar ya kuma jaddada cewa; Za a sake gina wannan garin, kuma yin hakan nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatin Lebanon.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Shin Kwankwasiyya ta kama hanyar wargajewa ne?

A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu. 

An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo.

Sai dai ba kowa ne ya san asalin mafarin rigimar ’yan majalisar da madugunnKwankwasiyyam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba.

Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.

 

Yadda kasuwar buƙata ta haɗe su da Kwankwaso a 2023

Dama dai ana ganin Sani Rogo da Kawu Sumaila, asali ba su da gami da tafiyar siyasar Kwankwasiyya, amma saboda kasuwar buƙata ce, suka haɗe daga baya.

Abdullahi Sani Dogo ya koma jikin Kwankwaso ne tun bayan raba gari da tafiyar gidan Malam Ibrahim Shekarau.

Shi kuma Kawu Sumaila, ya koma jikin Kwankwaso ne gab da zaɓen 2023.

Kabiru Alasan Rurum, asali ɗan Kwankwasiyya ne, amma ya bart a a lokacin Gwamnatin Ganduje, har ya zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano. Sai dai bayan hana shi takarar gwamna a Jam’iyyar APC, ya koma gidansa na da, wato Kwankwasiyya.

Wanda aka fi yin mamakin saɓaninsa da tsarin Kwankwasiyya shi ne Ali Sani Madakin Gini, ganin yadda a zamanin Ganduje, ya rasa kujerar ɗan Majalisar Tarayya saboda nuna biyayya ga Kwankwaso.

 

Ainihin tushen saɓaninsu da Kwankwaso

Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso da kansa ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli, ba tare da bai wa ɗaya da cikin waɗannan jiga-jigai dama ba.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa, babu wanda aka bai wa dama a cikinsu a fitar da shugabancin ƙananan hukumomin da suka fito, abin da suke ganin tamkar cin fuska ne ga buwayarsu ta siyasa.

Misali da ƙaramar hukumar Sumaila, a yadda aka saba, Kawu Sumaila shi yake kafa shugabanci a matakin ƙaramar hukumar, amma a wannan karon, Kwankwaso ya bai wa Faruk Abdu, ɗan tafiyarsa na asali, wanda kuma bai cika shiri da Kawu Sumaila ba a siyasance.

Tun daga lokacin ake zaman doya da manja, har ake zargin ’yan majalisar da ƙara rura wuta a tafiyar Abba Tsaya da Kafarka da ta kunno kai a kwanakin baya.

 

Makomar siyasar Kwankwasiyya

A yanzu haka, ’yan majalisar da aka dakatar sun barranta kansu da NNPP mai littafi, inda suka bayyana cewa, su ’yan Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ne. Kuma a yanzu haka maganar tana kotu, kan wane ɓangare ne ke da halaccin a matsayin jam’iyya.

’Yan Kwankwasiyya a Kano na kallon ’yan majalisar huɗu a matsayin masu butulci. Misali da Kawu Sumaila da ya daɗe yana neman Sanata bai samu ba, har sai da ya haɗa tafiya tare da Kwankwaso.

Ana ganin Kwankwasiyya ka iya samun rauni, musamman a Kano ta Kudu, idan har aka tafi a haka. Kuma da ma tun a zaɓen 2023, Kwankwasiyya ba ta da ƙarfin a-zo-a-gani a yankin Kano ta Arewa.

Abun jira a gani shi ne ko Kwankwaso zai yafe wa ’yan majalisar, a tunkari zaɓen 2027 tare, tun da dai siyasa kasuwar buƙata ce.

Ko kuma zai zaɓi zama shi ƙadai gayya a zaɓe mai zuwa, kamar yadda ya sha gwadawa a baya tana kai masa.

Idan ko hakan ya zaɓa, tabbas za a doka siyasa, kuma a cikin biyu a yi ɗaya: Walau ya koya musu darasinta, ko kuma su nuna masa ƙarfinsu ya kawo.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Masallacin Juma’a A Garin Samamiya Da Ke Birnin Kudu
  • Hukumar Lamuni Ta Duniya IMF Da Bankin Duniya Sun Ce Bazasu Taimakawa Lebanon Ba Sai Da Sharudda
  • An Yi Jana’izar Shahidan kungiyar Hizbullah Fiye Da 120 Kudancin Kasar Lebanon A Yau Jumma’a
  • A gaban mijina Akpabio ya fara neman kwanciya da ni —Sanata Natasha
  • Kwara ta Raba Littafai Fiye da Dubu 74 Kyauta Ga Dalibai
  • Shin Kwankwasiyya ta kama hanyar wargajewa ne?
  • Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa
  • Majalisar Dattijan Aljeriya Ta Soke Duk Wata Hulda Da Majalisar Dattijan Faransa
  • Sheikh Na’im Kasim Ya Gana Da Ministan Harkokin wajen Kasar Iran Da Shugaban Majalisar Dokoki