Wasu Kasashen Musulmi Sun Fara Azumin Ramadana A Yau Asabar, Yayin Da Wasu Za Su Fara A Gobe Lahadi
Published: 1st, March 2025 GMT
Daga cikin Kasashen da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya.
Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan.
A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan.
A nan Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon watan Ramadana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Watsi Da Barazanar HKI
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya.
Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba kaiwa Iran hari a bay aba kuma ba zata taba kai mata hari ba.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya buga wannan labarin a jiya Asabar ya kuma nakalto ministan yana cewa kasashen Rasha da Iran basu taba karfafa dangantakar tsakaninsu fiye da yanzu ba.
Aragchi ya kara da cewa kasashen Iran Rasha da kuma China suna aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a duniya a cikin yan shekarun da suka gabata. Kuma kasashen da gaske suke a kan hakan.