HausaTv:
2025-03-01@14:31:17 GMT

Yemen Ta Ce A Shirye Take Ta Koma Yaki Idan Yaki Ya Sake Barkewa A Gaza

Published: 1st, March 2025 GMT

Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2025.

Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bayyana cewa birnin Tel’aviv wato Yafa, zai zama babban wurin da makaman kungiyar zasu nufi idan hakan ya faru.

Huthi ya ce “Idan yaki ya sake barkewa za mu kai hare-hare a ko ina a HKI sannan birnin Tel’aviv zai za ma babbar manufar makamammu.

Yace: Kasar Yemen ta na kallom yadda al-amura suke tafiya a ayyukan tsagaita wutar, kuma ta na kallon yadda HKI take sabawa wasu abubuwan da ke cikin yarjeniyar. Ya kuma ambaci yadda HKI ta ki janyewa daga rafah da kuma yankin philidelfiya na kan iyaka da kasar Masar. Wanda kuma ya sabawa yarjeniyar. Sannan ya kammala da cewa gwamnatin kasar Amurka ta na kodaitar da HKI da yin hakan.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Musayar Yawu A Tsakanin Shugabannin Kasashen Amurka Da Ukiraniya A Fadar White House

Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya.

Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky yake Magana akan wasu sharudda kafin hakan ta faru.

Shugaban kasar Amurkan ya yi wa shugaban kasar Ukiraniya goron cewa, kasarsa ce take ba su taimakon kudade da makamai, yana mai kara da cewa; Ko dai ya amince da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin ko kuma Amurka ta dakatar da duk wani taimako.

Haka nan kuma shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukiraniya da cewa, yana son kunna wutar yakin duniya na uku,alhali bai taki komai ba.

Shi kuwa mataimakin shugaban kasar Amurka ya zargi Zylenisky da cewa , babu girmamawa ga Amurka da shugaban kasarta a cikin abinda yake yi..”

Shi kuwa shugaban kasar ta Ukiraniya ya ce, babu yadda za ayi , ya yi sasauci a gaban Putin na Rasha.”

Shugaban na Ukiraniya ya fice daga fadar White House ba tare da gabatar da taron manema labaru ba, kamar yadda tun da fari a ka tsara za a yi.

Bayan tafiyar tashi ne dai shugaban Amurka ya wallafa sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana cewa: Zylinesky ya wulakanta Amurka, amma zai iya dawowa idan ya shirya karbar zaman lafiya.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yi Musayar Yawu A Tsakanin Shugabannin Kasashen Amurka Da Ukiraniya A Fadar White House
  • Hukumar Lamuni Ta Duniya IMF Da Bankin Duniya Sun Ce Bazasu Taimakawa Lebanon Ba Sai Da Sharudda
  • An Yi Jana’izar Shahidan kungiyar Hizbullah Fiye Da 120 Kudancin Kasar Lebanon A Yau Jumma’a
  • Shugaban Hafsan Sojan Sama Na Najeriya Ya Zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama Na Afrika
  • NAFDAC Ta Kaddamar Da Sabbin Shirye-Shiryen Yaki Da Jaribun Magunguna
  • Masar Ta Yi Watsi Da Shawarar Cewa Ta Karbi Ragamar Gaza Na Wucin Gadi
  • Jami’an Diblomasiyyar Kasashen Rasha Da Amurka Zasu Sake Haduwa A Birnin Istambul A Gobe
  • Sheikh Na’im Kasim Ya Gana Da Ministan Harkokin wajen Kasar Iran Da Shugaban Majalisar Dokoki
  • Hamas Tace An Cimma Matsaya Da HKI Bayan Tsekon Da Aka Samu Na Sakin Fursinoni Falasdinawa 620