Iran Ta Zama Zakara A Damben Gargajiya Ta 2025 UWW Wanda Aka Gudanar A Kasar Albaniya
Published: 1st, March 2025 GMT
Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla.
Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a wannan wata a fagen kasa da kasa.
An gudanar da gasar ne a ranakun 27-28 na watan Fabrayrun wannan shekara, wato 2025UWW, wanda ya jawo hankalin masu shaawar wasan a duniya.
Daga cikin yan wasan da suka sami lambar zinari sun hada har da Ali Momini mai nauyin (57) Rahman Amouzad (65) Kamran Ghasempour da kuma Amir Hussain Zare.(125).
Sai kuma mai lambar Azurfa, wato Erfan Alizadeh (97). Younes Emami (74kg) ya sami tagulla. Iran ta sami maki 97 sai kuma kasar Japan wacce ta zo na biyu da maki 93.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Yakin Neman Zabe A Kasar Gabon
Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan daga baya ya sauka don ya sake dawowa da hanyar zabensa ya fara yakin neman zabe a jiya, inda yake kira ga mutanen kasar su zabe shi saboda kyautatuwar kasar Gabon.
A cikin watan Augustan shekara ta 2023 ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo wanda ya gaji babansa Umar Bongo bayan rasuwarsa ba tare da zabe ba.
A halin yanzu dai yan takara 8 ne suke neman wannan kujerar a zaben ranar 12 ga watan Afrilu. Idan ba’a sami wanda ya lashe zaben ba za’a sake gudanar da zabe tsakanin wadanda suka zo na daya da kuma na biyu a zagayen farko.
Shugaban kasa a Gaban, yana yin shugabnci na tsawon shekaru 7 a zagaye na farko idan ya sake tsayawa ya kuma ci zabe yayi zagaye na 2 wanda zai kaishi ga shekari 14 na shugabaci. Daga nan shi ba zai tsaya ba, kuma wani daga cikin danginsa ba zai tsaya ba.