A Yau Ce Dokar Haramta Amfani Da Tankunan Mai Masu Daukar Lita 60,000 A Najeriya
Published: 1st, March 2025 GMT
A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar.
Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA)’ ta haramta amfani da iran wadannan tankunan man ne daga yau Asabar 1 ga watan Maris, saboda ceton rayukan mutanen kasar.
Dokar ta kara da cewa, daga yau tankunan man masu daukar lita 45,000 zuwa kasa ne kawai za’a a barisu dauki man fetur zuwa wasu wurar daga deport.
Sai kuma kungiyar masu dakon man fetur a kasar sun bayyana cewa zasu yi asarar tankuna na kimani naira biliyon 300 saboda wannan haramcin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tsofaffin Ma’aikatan FRCN Zasu Ziyarci PTAD Don Neman Biyan Haƙƙoƙi
Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ma’aikatan FRCN, Alhaji Ibrahim Ahmad Jikamshi, zai jagoranci wata tawaga ta musamman domin ganawa da Babban Sakataren Hukumar PTAD kan muhimman batutuwa fansho da ta shafi tsofaffin ma’aikatan.
Alhaji Ibrahim Jikamshi dayake bayani a Kaduna, yace za a gudanar da wannan ganawa a cikin wannan mako domin tattaunawa kan wasu matsaloli da aka gano wajen biyan bashin da ake bin tsofaffin ma’aikatan shekaru da dama.
Ya tabbatar da cewa ƙungiyar tana ƙoƙari wajen shawo kan irin waɗannan matsaloli da suka dade ana fama da su, tare da fatan cewa hukumar PTAD za ta nuna gaskiya, rikon amana da kuma jajircewa wajen biyan hakkokin da suka rage.
Alhaji Ibrahim Jikamshi, wanda ya tunatar da matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka a baya na biyan bashin da ake bin tsofaffin ma’aikata ta hanyar sakin biliyoyin Naira, ya nuna damuwa da cewa har yanzu wannan mataki bai haifar da gamsasshen sakamako ba ga waɗanda abin ya shafa.
SULEIMAN KAURA