Haleyen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (1)
Published: 1st, March 2025 GMT
Dabi’un Da Suke Sa Malamin Makaranta Ya Ke Zama Nagartacce
Ko dai su kasance suna koyar da manyan dalibai ne ko kuma lamarin ya zama suna koyar da kirga ce daga daya zuwa goma Azakakuran Malamai suna da wadansu dabi’u da suka yi kama da juna. Alal misali sanin kowa ne duk dai masu ilimi ko masu harkar koyarwa suna da wata baiwa da tsayawa su saurarar maganar da ake fada/abin kuma ba ya tsaya kan lamarin dalibansu kadai ba,har ma abokan aikinsu, masu makarantu,da kuma iyayen daliban.
Kamar yadda bayanan Robert Lee, Ed.D., Shugaban Kwalejin ilimi ta Sanford dangane da hakan cewa yayi, “Abin so ne ace yana dabi’u da suka hada da babban abinda aka fi so shi ne ya kasance yana nau’oin basiru na iya mu’amala kwarai da gaske, tausayi, da kuma kauna da sha’awar aikin na koyarwa. Irin wadannan dabi’un ba kawai sun tsaya bane kan samar da hanyoyin / dabarun koyarwa masu kyau ba, akwai saw a dalibai son sun maida hankali kan abinda ake koya masu har ma akwai kai su ga hanyar samun nasarar karatu.Malamai wadanda suka san abinda suke yi suna da dabara ko halayya ta ta gane/ sanin darasin da suke koyarwa bugu da kari kuma sun san yadda za su koyawa dalibansu darasin ta hakan ne kuma zai zama masu abin alkhairi gare su. Ya kamata Malamai su rika karawa dalibansu kwarin gwiwa har sai ga sun kai iyakar mizanin da suke son zuwa ko kuma burinsu na karatu/,inda za a lura da kowane dalibi ana yi ma sa kallon yana da kima ta bangaren karatu/ilimin da suke bukata, suna girmmama kowa, yayin da su kuma ana ganin mutuncinsu/ girmansu.”
Duk da haka dai wasu dabi’un da ake bukata daga Malaman makaranta wasu ba su kai darajar wasu ba idan aka kalli amfanin da za a iya samu, wasu kuma da akwai matukar wuya idan ana son aiwatar da su, dukkan su dai suna da amfani ga Malamai ya zama sun sansu suna kuma aiwatar da su a harkar su ta koyarwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Hamayyar Siyasar A Kasar Turkiya Suna Ci Gaba Da Yin Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
A jiya Asabar dubun dubatar ‘yan hamayyar siyasa su ka yi gangami a birnin Stanbul bayan da jam’iyyar “National Party” ta gayyace su, domin ci gaba da yin tir da kamun da aka yi wa Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin na Stanbul.
Shugagan jam’iyyar “Turkish National Party’ ta adawa, Uzgur Ozil ya bayyana cewa adadin wadanda su ka halarci gangamin sun kai miliyan 2.2.
Daga cikin mahalarta gangamin da akwai mata da mahaifan Akram Ima wadanda su ka rika bayar da taken cewa za a ci gaba da yin gwgawarmaya ako’ina.”
Tun da asubahin jiya Asabar ne dai mutane su ka fara yin tururuwa a cikin birnin na birnin Sitanbul suna dauke da tutocin turkiya da kuma hotunan Mustafa Kamal Ataturk wanda ya kafa jamhuriyar Turkiya.
Tun bayan da aka kama Imam Uglu a ranar 19 ga watan Maris ne dai kasar ta Turkiya ta fada cikin dambaruwar siyasar wacce an dade ba a ga irinta ba.
Shugaban jam’iyyar hamayyar ya fadawa jaridar “ Lo Monde” ta Faransa cewa a kowace Asabar za su zabi garin da za su gudanar da Zanga-zanga,sannan kuma da kowane marecen Laraba a cikin birnin Sitanbul.