Aminiya:
2025-03-01@15:05:41 GMT

Ramadan: ’Yan sanda sun tsaurara tsaro saboda azumi a Borno

Published: 1st, March 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan.

Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma.

Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kammala shirin tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin watan Ramadan.

“Mun san muhimmancin wannan wata ga ’yan uwanmu Musulmi,” in ji sanarwar.

“Saboda haka, mun ƙara sintiri da samar da jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.”

Kwamishinan ’yan sandan Borno, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya tabbatar da cewa rundunar tana sadaukar da kai domin kare lafiyar jama’a a cikin wannan wata.

“Burinmu shi ne kowa ya samu damar gudanar da ibadarsa cikin kwanciyar hankali da tsaro,” in ji Kwamishinan.

Haka kuma, rundunar ta buƙaci jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

“Idan kun ga wani abu, ku sanar da hukuma,” in ji ASP Daso.

Rundunar ta kuma fitar da lambobin kiran kar ta kwana domin bayar da rahoto: 08068075581 da 08023473293.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ramadan Tsaro rundunar ta

এছাড়াও পড়ুন:

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025.

Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labara.

Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Ramadan ya sanar da hakimi ko uban ƙasar da ke kusa da shi.

Daga nan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da suke yi na addini.

Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, kuma al’ummar Musulmi na azumtar sa baki ɗaya.

Azumin Ramadan shi ne ka uku a cikin ginshikan addinin Musulunci guda biyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mece Ce Makomar ‘Ramadan Basket’ A Wannan Lokaci Na Matsin Tattalin Arziki?
  • Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno
  • An ga watan Ramadan a Najeriya — Sarkin Musulmi
  • An ga watan Ramadan a Najeriya —Sarkin Musulmi
  • An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya 
  • Bankin Raya Afirka ( AFDB) Ya Bayyana Kasashen Da Tattalin Arzikinsu Yake Bunkasa Da Sauri A Cikin Nahiyar
  • Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan
  • Sarkin Moroko Ya Buƙaci Yan Kasar Kada Su Yi Layya A Bana
  • Ɗangote Ya Rage Farashin Man Fetur Saboda Gabatowar Azumi