Gobara Ta Sake Ƙona Kasuwar Kara A Sokoto
Published: 1st, March 2025 GMT
Wata gobara ta sake tashi a fitacciyar Kasuwar Kara da ke Sokoto, wacce aka fi sani da sayar da hatsi da kayan abinci, inda ta cinye gaba ɗaya kasuwar tare da mayar da shaguna da wuraren ajiyar kaya toka.
Gobarar ta fara ci ne da safiyar Asabar, inda jami’an kwana-kwana suka yi ƙoƙarin shawo kanta amma ta gagara.
A halin yanzu, masu shaguna da gidaje da ke kusa da kasuwar na kwashe kayansu saboda tsoron sake ɓarkewar wutar. Hukumar kasuwar ba ta samu damar yin jawabi ba domin suna ƙoƙarin hana mutane yin amfani da iftila’in don yin sata.
A baya-bayan nan, wani ɓangaren kasuwar da ake amfani da shi wajen niƙa ya kone ƙurmus, inda gwamnatin jihar ta alkawarta tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gobara
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji Kan Kayayyakinta
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp