HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato
Published: 1st, March 2025 GMT
Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato.
Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi.
An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin ArewaWani ɗan kasuwar da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun da misalin ƙarfe 6:30 amma sai wurin ƙarfe 3:30 na rana aka samu nasarar kashe ta.
A cewarsa, gobarar ta yi ta’adi a ɓangaren shagunan masu sayar da abinci da suka haɗa da gero, dawa da masara da shinkafa.
Haka kuma, majiyar ta ce wutar ta yi ɓarna a ɓangaren masu ƙyamare da layin maƙera da masu maganin gargajiya.
“A ƙiyasi an yi asarar kuɗi za su kai Naira miliyan 500 domin dukkan shagunan da gobarar ta taɓa sun ƙone ƙurmus, masallaci ne kawai abun bai shafa ba.”
Ya buƙaci gwamnati da ta jingine batun siyasa a gefe wajen kafa kwamitocin da take ɗora wa alhakin bibiyar wannan ibtila’i domin ɗaukar matakan da suka dace bisa adalci.
Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku cikin ƙasa da shekara ɗaya da ake samun tashin gobara a kasuwar.
Ya nanata kiran cewa bayan jajanta wa ’yan kasuwa akwai kuma buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin kare dukiyar mutane daga irin wannan hasara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Jihar Sakkwato Kasuwar Kara
এছাড়াও পড়ুন:
Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Duniya Ya Kara Fito Da Kyawun Kasuwar Sin
Kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, don haka masu zuba jari na kasashen waje za su gane wa idonsu irin damammakin da aka samar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp