Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa
Published: 1st, March 2025 GMT
Allah Ya yi wa Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan shafe shekaru 125 a duniya.
Fadar Sarkin Sasa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ce ta bayar da sanarwar rasuwar Sarkin wanda ke riƙe da muƙamin Sardaunan Yamma.
HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a YobeBayanin rasuwar Sarkin Sasa yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ɗan Masanin Sasa, Alhaji Kasim Ado Yaro ya raba wa manema labarai a ranar Asabar.
Ɗan Masanin na Sasa ya ce Alhaji Maiyasin ya rasu ne a yau Asabar bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Ibadan.
Sarkin Sasa wanda kuma yake riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudancin Nijeriya ya rasu ya bar mata 2 da ’ya’ya bakwai.
Sanarwar ta ce za a yi jana’izar Alhaji Haruna Maiyasin a gobe Lahadi.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a shekarar 1981 ce aka naɗa Alhaji Haruna Maiyasin a matsayin Sarkin Sasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa wani muhimmin abu da ba za a iya mantawa da shi a tarihin marigayin ba shi ne taimakon bayin Allah da kyautar kuɗi da kayan abinci da suturu bayan aikin jagorancin jama’a da ya sanya a gaba a lokacin yana raye.
Fitowa cikin jama’a ta baya bayan nan da Sarkin Sasa ya yi ita ce lokacin da ya jagoranci manyan Fadawansa zuwa ofishin Gwamnan Jihar Oyo da ke Agodi domin yi wa Gwamna Seyi Makinde ta’aziyar rasuwar yayansa watanni biyu da suka gabata.
Aminiya ta ruwaito cewa yanzu haka Sarakunan Hausawa da Fulani na kusa da birnin Ibadan da manyan malaman Addinin Musulunci suna sun fara zaman makoki a gidan marigayin da ke Sasa zuwa gobe Lahadi da za a yi masa jana’iza.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alhaji Haruna Maiyasin Jihar Oyo Sarkin sasa Sarkin Sasa
এছাড়াও পড়ুন:
Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano
Sarkin tare da tawagarsa sun fita a ciki jerin gwanon motoci zuwa gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tarbe su.
Bikin bana ma ya sha bamban da na baya, domin an sauya hanyoyin da ake bi a baya.
Duk da hakan, jama’a da dama sun fito suna murna da jin daɗi yayin da motocin Sarkin ke wucewa.
Duba hotunan hawan a ƙasa:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp