Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombia sun jaddada aniyarsu ta hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila amfani da tashar jiragen ruwansu, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi a zirin Gaza.

“Za mu hana jiragen ruwa da ke dauke da kayan aikin soji zuwa Isra’ila amfani da tashoshin jiragen ruwanmu; kamar yadda,” Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Firayim Ministan Malaysia Anwar Ibrahim da Shugaban Colombia Gustavo Petro suka rubuta a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da mujallar harkokin waje ta buga a wannan makon.

Sun jaddada cewa yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya fallasa gazawar tsarin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen rashin hukunta dokokin kasa da kasa da Isra’ila ke yi.

Malesiya da Colombia na daga cikin kasashen da suka goyi bayan korafin kisan kiyashin da kasar Afrika ta kudu ta kai kan Isra’ila a kotun duniya ta ICJ.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas Ta Yi Watsi Da Shawarar Isra’ila Na Tsawaita Matakin Farko Na Tsagaita Wuta A Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko.

Yau Asabar ne dai matakin farko na yarjejeniyar ke kaow karshe.

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Al Araby cewa, ba za a amince da tsawaita matakin farko na yarjajjeniyar kuma gwamnatin mamaya na da cikakken alhakin gazawar fara shawarwari a mataki na biyu na tsagaita wuta a zirin Gaza.

Qassem ya kuma lura da cewa, maganar da Isra’ila ta yi na tsawaita kashi na farko na da nufin kwato sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin Isra’ila tana kaucewa kudurinta na kawo karshen yakin da kuma ficewa daga zirin Gaza gaba daya.

Qassem ya ci gaba da cewa, babu wata tattaunawa a halin yanzu na wani mataki na tsagaita bude wuta a Gaza da kungiyar Hamas, yana mai jaddada cewa dole ne a fara tattaunawa a mataki na gaba da nufin samar da tsagaita wuta ta dindindin.

Ya kuma bukaci masu shiga tsakani da kasashe masu bada garantin da su tursasa gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar a dukkan matakanta, sannan ta shiga mataki na biyu ba tare da wani shakku ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas: Matakin Netanyahu na hana shigar kayan agaji a Gaza keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne
  • Kasashen Somaliya Da Habasha Suna Gab Da Rattaba Hannu Akan Amfani Da Tashar Jirgin Ruwa
  • Hamas Ta Yi Watsi Da Shawarar Isra’ila Na Tsawaita Matakin Farko Na Tsagaita Wuta A Gaza
  • Noman Rani: Tinubu Ya Amince Da Fadada Madatsun Ruwa 12 A Nijeriya
  • Kasashen Afrika Ta Kudu, Malasiya Da Colombia Zasu Hana Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Tsayawa A Tashoshin Jiragen Ruwansu
  • Kwastam Da Hukumar NPA Sun Kulla Hadakar Bunkasa Ingancin Aiki A Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Wata Mujalla Ta Zabi Shugaban NPA A Matsayin Gwarzonta Na Shekarar 2025
  • Pezeshkian: Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Kara Karfafa Alakokinsu
  • An kori ma’aikatan Microsoft saboda adawa da yahudawan sahyoniya