Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza.

Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya.

»

Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. »

Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga yankin Rafah. »

Al-Houthi ya kara da cewa: Haka nan makiya yahudawan sahyoniya ba su janye gaba daya daga kudancin kasar Labanon ba, wanda ya zama mamaya da kuma barazana ga al’ummar kasar Lebanon da kuma keta  hurimin kasar. »

Zamu zura ido mu gani, kuma dole ne mu kasance cikin shiri,” in ji jagoran kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sharhi:  Kalankuwar  Kona Rayayyu Da Wuta A Gaza

Sojojin mamayar HKI sun fara aiwatar da wani sabon kisa ta hanyar amfani da sabon salo akan Falasdinawa. Kai kace tsawon watanni 18 da su ka dauka suna amfani da makamai mabanbanta wajen kashe mutanen Gaza, bai isha sun cimma manufofin da su ka Sanya a gaba.

Sabon salon kisa wanda  ya yi kama da “Kalankuwar Masu Cin naman mutum” bayan sun soya shi, shi ne abinda yake faruwa.

 Isra’ila ta kai hari da jirgin yakin maras matuki na kunar bakin wake akan sansanonin ‘yan hijira da su ka yi dandazo a wuri daya. Iyalan Abur-Rus ne wannan jirgin kunar bakin waken ya fada a kansu  ya kashe da dama daga cikinsu ta hanyar kona su da ransu. Mutane 20 ne su ka kone kurmus a cikin wadannan iyalan na Abu-Rus.

A daidai lokacin da daruruwan mazauna wannan sansanin ‘yan hijirar su ka taru domin su kashe wutar da harshenta ke toroko da tashi sama, jikin iyalan Rus yana ci gaba da konewa har su ka yi shahada ba tare da an iya ceto su ba.

Bayan da wuta ta lafa, sauran danginsu da su ka saura da su ka zo daga nesa, sun dauki sa’oi ba tare da sun iya tantance wane da wane ba.

Wannan salon kisa na kone Falasdinawa da ransu, bai tsaya a cikin iyalan Abur-Rus ba, Isra’ila ta sake aike wa da wani jirgin saman maras matuki na kunar bakin wake zuwa wani sansanin ‘yan hijirar.  Wannan karon a unguwar “Razana” dake Beit-Lahiya a Arewacin zirin Gaza. Shi ma jirgin kunar bakin waken ya fada kan hemar iyalai guda da su ka kunshi Uba, Uwa, da ‘ya’yansu 4 tare da kone su kurmus.

 Kafin akai abinda ya saura na gangar jikin shahidai zuwa asibitin “Indonesia” dake Arewacin Gaza, wani jirgin sama maras matuki na kunar bakin wake, ya fada akan hemar wasu iyalan a sansanin ‘yan hijira na Jabaliya. A wannan karon iyalan “Asliyyah’ ya fada wa, ya yi sanadiyyar shahadarsu, su 7 baki daya. Sun kuwa kunshi kananan yara 5 da mahaifansu.

Da gari ya waye, mutanen sansanin ‘yan hijira na Jabaliya sun tashi da wani kisan kiyashin  akan makarantar Ayyubiyyah, dake karkashin hukumar Agaji. Wani jirgin maras matuki na ‘yan mamaya ya kai harin kunar bakin wake akan  wannan makaranta a daya daga cikin dakuna, da ya yi sanadiyyar shahadar ‘yan hijira 6 da kuma jikkatar wasu gwammai.

 **

A daidai wannan lokacin da HKI take shan jinin Falasdinawa ta hanyar kona su a raye, jiragen yakinta suna kai wasu hare-haren  a gidan iyalan Najjar dake Jabaliya. An kuwa sami shahidai 3. Haka nan kuma sun kai wasu hare-haren  a wata gona a garin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 2.

Su ma manyan bindigogin HKI suna ci gaba da kai nasu hare-haren babu kakkautawa a sassa daban-daban na Gaza,musamman a unguwanni da suke gabashin birnin Gaza, da su ka hada ‘ al-tuffah’ shjaiyyah, da Sha’af da Beit Hanun.

Bai zama abin mamaki ba da hukumar lafiya ta duniya ( W.H.O) ta siffata Gaza da cewa ta zama “babbar makabarta”. Ta kuma kara da cewa; “Isra’ila tana kai wa hemomin ‘yan hijira hare-hare cikin sani, da kuma manufa.” Haka nan kuma hukumar ta ce; “Babu wani wuri wanda yake da aminci a cikin fadin Gaza”.Sannan ta kara da cewa; An hana ta shigar da kayan agaji na magunguna da sauran kayan aiki na likitanci saboda tarnakin da Isra’ila ta gindaya. Ta kuma Karkare da cewa; “Rashin abinci mai gina jiki a Gaza ta kai koli.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar kare farar hula ta Falasdinu ta zargi sojojin da ” kashe-kashe masu yawa”
  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • Wasu Falasdinawa Sun Yi Shahada A Harin Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Zirin Gaza
  • Gaza : Red Crescent ta yi watsi da rahoton Isra’ila kan kisan da aka yi wa jami’an agaji
  • Bikin Easter : Paparoma Francis ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
  • Sharhi:  Kalankuwar  Kona Rayayyu Da Wuta A Gaza
  • Kasar Rasha Ta Sanar Da Tsagaita Bude Wuta Da Ukraine Na Tsawon Kwanaki Bikin Ester
  • Putin ya umarci tsagaita wuta a Ukraine albarkacin bikin Ista
  • Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Mene Ne Shirin Nukiliya Na Iran Kuma Me Amurka Ke So Ta Yi?