Hamas Ta Yi Watsi Da Shawarar Isra’ila Na Tsawaita Matakin Farko Na Tsagaita Wuta A Gaza
Published: 1st, March 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko.
Yau Asabar ne dai matakin farko na yarjejeniyar ke kaow karshe.
Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Al Araby cewa, ba za a amince da tsawaita matakin farko na yarjajjeniyar kuma gwamnatin mamaya na da cikakken alhakin gazawar fara shawarwari a mataki na biyu na tsagaita wuta a zirin Gaza.
Qassem ya kuma lura da cewa, maganar da Isra’ila ta yi na tsawaita kashi na farko na da nufin kwato sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ya ci gaba da cewa gwamnatin Isra’ila tana kaucewa kudurinta na kawo karshen yakin da kuma ficewa daga zirin Gaza gaba daya.
Qassem ya ci gaba da cewa, babu wata tattaunawa a halin yanzu na wani mataki na tsagaita bude wuta a Gaza da kungiyar Hamas, yana mai jaddada cewa dole ne a fara tattaunawa a mataki na gaba da nufin samar da tsagaita wuta ta dindindin.
Ya kuma bukaci masu shiga tsakani da kasashe masu bada garantin da su tursasa gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar a dukkan matakanta, sannan ta shiga mataki na biyu ba tare da wani shakku ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu Falasdinawa Sun Yi Shahada A Harin Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Zirin Gaza
Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza
Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma yana gudanar da wannan ta’asa ne tare da goyon bayan siyasa da na sojan Amurka, sannan kungiyoyin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashe sun daukin matakin yin shiru da rashin gwada wani yunkurin kalubalantar wannan danyen aiki.
Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama tare da rusa gidaje, gami da karfafa haramcin shigar kayan abinci ga Falasdinawa tun farkon watan Maris da ya gabata. Wannan ya kara janyo bullar masifar yunwar da al’ummar Zirin Gaza ke fuskanta.